Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2024

Haifaffen Ka'aba!

Haifaffen Ka'aba shine Imam Ali (AS), masadir dayawa na shi'a da sunni sun ruwaito wannan hadisa da ta faru na haihuwan Imam Ali (AS) a cikin ɗakin Allah, a ranar 13 ga watan Rajab. Allama Majilisi ya naƙalto masadar 16 na sunni da suka hakaito wannan hadisa, haka nan ya naƙalto masadir 50 na shi'a da suka kawo hadisar, shi yasa hadisan haihuwar Imam Ali (AS) a cikin Ka'aba sun kai haddin tawatir. Sadouq ya ruwaito a littafin sa الأمالي والمعاني الأخبار daga Zaidu bin Ƙa'anab yace: "Na kasance zaune tare da Abbas bin Abdulmutallib a jikin ɗakin Ka'aba sai muka ga Faɗimatu bintu Asad ta tunkaro tana ɗauke da juna, tana cewa : Ya Allah hakika ni mai imani ce da kai, da abinda ƴan aiken ka suka zo da shi na daga litattafai, kuma ni mai gaskata maganganun kakana Ibrahim khalil ce, don wanda ya gina wannan ɗaki, don wannan abin haihuwa da ke cikina ka sauƙaƙa min haihuwa ta, Yazid yace: Nan take muka ga ginin ɗakin Ka'aba yana tsagewa, sai Faɗima...