Skip to main content

Haifaffen Ka'aba!

Haifaffen Ka'aba shine Imam Ali (AS), masadir dayawa na shi'a da sunni sun ruwaito wannan hadisa da ta faru na haihuwan Imam Ali (AS) a cikin ɗakin Allah, a ranar 13 ga watan Rajab.

Allama Majilisi ya naƙalto masadar 16 na sunni da suka hakaito wannan hadisa, haka nan ya naƙalto masadir 50 na shi'a da suka kawo hadisar, shi yasa hadisan haihuwar Imam Ali (AS) a cikin Ka'aba sun kai haddin tawatir.

Sadouq ya ruwaito a littafin sa الأمالي والمعاني الأخبار daga Zaidu bin Ƙa'anab yace: "Na kasance zaune tare da Abbas bin Abdulmutallib a jikin ɗakin Ka'aba sai muka ga Faɗimatu bintu Asad ta tunkaro tana ɗauke da juna, tana cewa : Ya Allah hakika ni mai imani ce da kai, da abinda ƴan aiken ka suka zo da shi na daga litattafai, kuma ni mai gaskata maganganun kakana Ibrahim khalil ce, don wanda ya gina wannan ɗaki, don wannan abin haihuwa da ke cikina ka sauƙaƙa min haihuwa ta, Yazid yace: Nan take muka ga ginin ɗakin Ka'aba yana tsagewa, sai Faɗimatu bintu Asad ta shiga ciki, sai ginin ɗakin ya haɗe" Munyi ƙoƙarin buɗe kwaɗon da ke kofar ɗakin amma yaƙi buɗuwa, tsawon kwanaki huɗu Faɗimatu bintu Asad tana ciki sannan ta fito tare da ɗanta"

Abune sananne ɗakin Ka'aba yana da ƙofa da ake iya shiga ko fita daga cikinsa, amma a lokacin da ta yi addu'ar ba ƙofar ne ya buɗu ba, ginin ne ya tsage, a nan Allah na so ne ya nuna maka saɓanin al'ada Mu'ujiza, saboda kada wata rana a samu wani da zaice ai iska ne ya tura kofar shi yasa ta buɗe.

Babban Abin Mamakin Shine: Har zuwa yau alamun tsagewan yana jikin ɗakin ka'aban, duk da sake ginin da aka sha yi tsawon ƙarnoni da duka gabata, kuma kafinsa da bayansa ba'a samu wani da aka haifa a cikin Ka'aba ba.

Tsawon kwanakin da ta yi a cikin ɗakin Imam Ali (AS) bai kama nono ba, baici komai ba kuma idanu a rufe, sai ranar da ta fito Annabi Muhammad (S) ya zo ya karɓe shi sannan ya buɗe idanu, farkon wanda Imam Ali (AS) ya yi tozali da shi shine Annabi Muhammad (S), sannan Annabi ya sanya harshensa a cikin bakin Imam Ali (AS), Imami ya rinƙa tsotsa, Allah kaɗai ya san sirrukan da ya tsotsa.

Ina taya ɗaukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwansa Haifaffen Ka'aba Imam Ali (AS), wanda ya faru a 13 ga watan Rajab.

24/01/2024,
Emran Darussalam.

Comments

Popular posts from this blog

Muhimmancin Ranar Arfa A Imamiyya.

Da Alƙalamin Sheikh Imrana Darussalam  Azumin Arfa (ranar 9 ga Zul-Hijja) yana da matsayi mai girma a tsarin ibada na Imamiyya (Shi'a), kodayake yana da bambanci kadan da fahimtar Ahlus-Sunna. A mad'hab din Imamiyya, wannan rana tana da daraja ta musamman saboda kasancewarta rana mai tsarki, rana ta addu'a da tuba, kuma rana ce da Allah ke gafartawa bayinsa da dama, musamman ga wadanda ke Arafat da kuma wadanda ba su je Hajji ba. 1. Muhimmancin ranar Arfa a Imamiyya Ranar Arfa ita ce rana ta biyu mafi falala a cikin shekara bayan Laylatul Qadr. Shi’a Imamiyya suna ganin cewa wannan rana ita ce ranar kusanci da Allah, inda ana karanta addu'o'i da yawa, musamman Addu'ar Imamu Husain (a.s) a ranar Arfa da kuma Addu’ar Imam Zainul Abidin (a.s), wadanda suka kunshi falsafa mai zurfi da ruhaniya mai karfi. 2. Azumi a ranar Arfa a Imamiyya Azumin ranar Arfa yana da falala mai girma ga wanda ba ya aikin Hajji, kamar yadda ya zo a hadisan Ahlul Bayt (a.s). Ha...

AYYUKAN DAREN FARKO NA WATAN RAJAB

Ayyukan daren farko na watan Rajab: 1– Wanka (Gusl): An rawaito daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Duk wanda ya samu watan Rajab, ya yi wanka a farkonsa, tsakiyarsa da ƙarshensa, zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” 2– Raya daren (ibada a daren): Wannan na daga cikin darare huɗu da ake ƙarfafa mustahabbancin rayar da su. An rawaito daga Abu Abdullahi (AS), daga mahaifinsa, daga kakansa, daga Ali (AS) cewa ya ce: “Yana so ya keɓe kansa a darare huɗu cikin shekara: daren farko na Rajab, daren tsakiyar Sha’aban, daren Idin Fitr, da daren Idin layya.” 3– Addu’a lokacin ganin jinjirin wata: اللّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلّيْنا بالأمْنِ وَالإيْمانِ وَالسَّلامَةِ وَالإسْلامِ رَبِّي وَرَبُّكَ الله عَزَّ وَجَلَّ. Kuma Manzon Allah (SAW) idan ya ga jinjirin Rajab yana cewa: اللّهُمَّ بارِكْ لَنا فِي رَجَبٍ وَشَعْبانَ وَبَلِّغْنا شَهْرَ رَمَضانَ وَأَعِنَّا عَلى الصِيامِ وَالقِيامِ وَحِفْظِ اللّسانِ وَغَضِّ البَصَرِ وَلا تَجْعَلْ حَظَّنا مِنْهُ الجُوعَ وَالعَطَشَ. Sal...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...