Skip to main content

Posts

Ina Ɗaliban Ilimi???

Ina Ɗaliban Ilimi??? Sheikh Muhammad Taƙi Bahjah (QS) yace: Ta hanyar ƙwarewa, ya zama abu sananne gare ni cewa: "idan ba'a sami sakaci a cikin lamuran ibada ba, to za a iya kammala darasin da ke bukatar yin awa ɗaya cikin mintuna goma! (tare da fahimta)"  Allah yana cewa: "Kuma kuji tsoron Allah da takawa, sai Allah Ya sanar da ku" – Baqarah, aya 282. Sharhi: Wato a yayin da bawa ya kula da janibin ibada tare da tsoron Allah, zai sami saurin fahimta a janibin karatu, zai fahimci karatu cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da shan wahala ba. 05/06/2024, Emran Darussalam
Recent posts

🌹✨ RANAR JADDADA MUBAYA'A DA ABOTA – RANAR GHADIR ✨🌹

🌹✨ RANAR JADDADA MUBAYA'A DA ABOTA – RANAR GHADIR ✨🌹 💚 Ɗan uwa zo Mu Sake Jaddada Abota da Ƴan'uwantaka Kan Wilayar Amirul Muminina Imam Ali (A.S.) 💚 🤝📜 Ni Emran Darussalam Ina cewa gare ka: "Na ƙaunace ka saboda Allah, na yi abota da kai saboda Allah, kuma na yi alkawari da Allah, Mala'ikunsa, Littattafansa, Manzanninsa da Imamai Ma'asumai (A.S.) cewa idan na kasance daga cikin mutanen Aljanna kuma aka ba ni izinin shiga Aljanna, ba zan shiga ba sai tare da kai." 💐 Ɗan uwa ka amsa da: ✨ "Na karɓa." ✨ 🤲 Sannan: "Na yafe maka dukkan haƙƙoƙin 'yan'uwantaka da ke tsakanina da kai, sai dai tabbatuwa a kan Wilayar Amirul Muminina Imam Ali (A.S.) da sauran Ahlulbaitin Tsira (A.S.), da kuma haƙƙin shafa'a, addu'a da ziyara." 💚❓ _Shin ka karɓa?_ ❓💚 🌺 Wannan wata kyakkyawar al'ada ce ta ranar Eidul Ghadir, wadda ke ƙarfafa zumunci, soyayya da haɗin kai saboda Allah. A wannan rana, mabiya Ahlulbaiti (A.S.) suna sabunta ...

Tarbiyya A Wajen Malaman Shi’a, Musamman A Mahangar Falsafar Tarbiyya Da Akhlāq A Fikirar Ahlul Bayt (a.s).

Tarbiyya A Wajen Malaman Shi’a, Musamman A Mahangar Falsafar Tarbiyya Da Akhlāq A Fikirar Ahlul Bayt (a.s). Tarbiyya tana nufin tsari na ilmantarwa da gina ɗan adam don isa zuwa ga kamala (Samun yardan Allah ) – wato kai mutum zuwa matakin da Allah Yake so, ta hanyar gyara Aƙida, ladubba, da halaye, da kuma shiryar da zuciya zuwa ga Ubangiji (Mahalicci). 🔹 Ma’anar “Tarbiyya” A Harshen Shi’a: Kalmar "Tarbiyya" tana nufin: "Nuna kulawa da gina mutum daga matakin ƙanƙanta zuwa manyanta, tare da ci gaba da tsare shi a kowane mataki na ci gaba – har ya kai ga kamala (Samun yardan Allah). Saboda haka, tarbiyya a mahangar Shi'a ba kawai koyar da ilimi ba ce, amma gyaran ruhi ne, halayya, da tunani, bisa koyarwar Qur’ani da Ahlul Bayt (a.s). Mahimmancin Tarbiyya A Makarantar Ahlul Bayt (a.s): 1. Tarbiyyar Imani: Tarbiyyantar da mutum a kan gaskata da kaɗaita Allah (tawhīd), Ma’ad (Makoma ƙiyama), Annabta, da Imama. Wannan shi ne tushen tarbiyya. 2. Tarbiyyar Akhlaqi (Halaye...

Ta Yaya Albarka Ke Ƙaruwa A Gida

Ta Yaya Albarka Ke Ƙaruwa A Gida?   Amirul Muminin Ali (a.s) ya ce: (Gidan da ake karanta Alqur'ani a cikinsa, kuma ake ambaton Allah Ta'ala, albarkarSa tana yawaita, Mala'iku suna halartarsa (cikin gidan), shaidanu suna barinsa, kuma (gidan) yana haskakawa ga mazauna sammai kamar yadda taurari ke haskakawa ga mutanen ƙasa, amma gidan da ba a karanta Alkur'ani a cikinsa, kuma ba a ambaton Allah, albarkarsa tana raguwa, kuma mala'iku suna barinsa, shaiɗani suna halartan gidan.  Masdar: Al-Kafi, juzu'i na 2, shafi na 499. 27/05/2024, Emran Darussalam

Kwaɗaitarwa Kan Azumin Ranar Arfa da Ayyukan Cikinta

Kwaɗaitarwa Kan Azumin Ranar Arfa da Ayyukan Cikinta Ranar Arfa tana daga cikin mafi girman ranaku a Musulunci, rana ce ta rahama, gafara, karɓar addu’a da kusanci ga Allah Maɗaukaki. Ita ce ranar tara ga watan Zul-Hijja, ranar da mahajjata suke tsayuwa a filin Arfa suna roƙon Ubangijinsu cikin tawali’u da kuka. An rawaito daga Manzon Allah (S.A.W) cewa azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekara biyu; shekarar da ta gabata da kuma mai zuwa. Wannan wata babbar dama ce ga masu neman gafarar Allah da tsarkake zukata. Falalar Azumin Ranar Arfa Azumin ranar Arfa na daga cikin ibadun da malamai suka yi matuƙar kwaɗaitarwa a kansa ga waɗanda ba sa aikin Hajji. Rana ce da: Allah ke yawaita ‘yanta bayinsa daga wuta. Addu’o’i suke samun karɓuwa. Rahama da albarka suke sauka. Zuciya take samun nutsuwa da kusanci ga Allah. Saboda haka kada mu bari wannan rana ta wuce ba tare da: azumi, addu’a, istigfari, salati ga Annabi da Ahlulbaitinsa (A.S), karatun Alƙur’ani, da yawaita ambaton Allah ba. M...

A Irin Wannan Rana Na 09 Ga Watan Aprilu Saddam Hussein Ya Kashe Yayi Shahid Sayyid Muhammad Baƙir Assadr (QS), Yau Shekaru 46.

A Irin Wannan Rana Na 09 Ga Watan Aprilu Saddam Hussein Ya Kashe Yayi Shahid Sayyid Muhammad Baƙir Assadr (QS), Yau Shekaru 46. Daga Kalamansa Na Hikima: 🌿 Akan ilimi Mutum bai kamata ya riƙe ilimi a matsayin abin da zai yi alfahari da shi ba, a’a ya kamata ya gan shi a matsayin nauyi da ke kansa na taimakon mutane da shiryar da su. 🌿 Akan sauyin al’umma Gyaran al’umma ba ya samuwa da magana kawai, sai an haɗa da aiki, haƙuri da sadaukarwa. Duk wanda yake son canji dole ya shirya wahala. 🌿 Akan mu’amala da mutane Hanyar da ta fi tasiri wajen gyaran mutane ita ce tausayi da kyakkyawar zuciya, ba tsauri da tsanani ba. 🌿 Akan jagoranci Jagora na gaskiya shi ne wanda yake ɗaukar alhakin mutane a zuciyarsa, yana damuwa da halin da suke ciki fiye da yadda yake tunanin kansa. 🌿 Akan gwagwarmaya Manyan nasarori ba sa zuwa cikin sauƙi, suna buƙatar ƙoƙari mai tsanani da sadaukarwa kafin a kai gare su. 🌿 Akan tsoron Allah Idan mutum ya gyara zuciyarsa tsakani da Allah, rayuwarsa gaba ɗaya ...

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan.

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan. A lokacin da Sayyid Muhammad Baƙir Sadr yake neman ilimi Ƙanwarsa Bintul Hudah tace: "Na kasance tare da ɗan'uwana a wancan lokacin muna tattara kuɗin da muke samu, koda kuwa kaɗan ne, sai Sayyid ya sayi littafi da su, mu karanta mu fahimta. Daga baya sai ya sayar da littafin domin ya sayi wani. Haka muka ci gaba da rayuwa bayan hijirarmu zuwa Najaf al-Ashraf" - Amma daga ƙarshe mai ya faru? Ilimin shi Sayyid Muhammad Baƙir Sadr (QS) da rubuce rubucen shi sun gajiyar da masu bincike, saboda duk wani mai ilimi da ya karanta littattafansa sai ya jinjina masa, ga kaɗan daga shaidan manyan Malaman Shi'a a kansa: - Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Abul Qasim Al-Khuʾi (QS) yace: "Lallai Najaful Ashraf tana alfahari da Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Lallai Allah Maɗaukaki Ya bai wa wannan Sayyid abin da bai ba wa wani ɗalibina ba." - Sayyid Ruhullah Al-Musawi Al-Khumaini (QS) yace: "Sayyid Muhammad Baqir Sadr yana daga cikin fitattun M...