Skip to main content

Posts

Showing posts from April, 2025

Fitinar Ƙarshen Zamani.

Ruwaya daga Abdullah bin Sinan, ya ce, Abu Abdillah Sadiq (A.S) ya ce: "Wani shubuha zai same ku, sai ku kasance ba tare da wani shugaba da ake iya gani ba, kuma ba tare da wani Imam mai shiryarwa ba, kuma babu wanda zai tsira daga gare ta sai wanda yake karanta du'aul gariyƙ Na ce: Yaya du'au Gariyƙ take? Sai ya ce (A.S): "Ya Allahu Ya Rahman Ya Rahim Ya Muƙallibal Ƙulub, Thabbit Ƙalbi Ala Dinik" 📚 Kamal ad-Din wa Tamam an-Ni'ima, as-Saduq, shafi na 380. 27/05/2025, Emran Darussalam.

Aikin Rana

Aikin rana shi ne haskakawa ko da tana bayan gajimare ne, haka ma Hujja (Atfs) aikin shi shine shiryarwa ko da yana boyayye ne gare mu a cikin hijabin ɓoyuwa (Gaiba), kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce. Idanunmu ba sa iya ganinsa, amma akwai wani rukuni na jama'a da suka rika ganinsa kuma har yanzu suna ganinsa; kuma ko da ba sa ganinsa (a yanzu) to suna da alaƙa da shi. Sheikh Muhammad Taƙi Bahja (QS).