Skip to main content

Posts

Showing posts from November, 2024

Komawa Ga Allah A Lokacin Tsanani.

Komawa Ga Allah A Lokacin Tsanani   Shin zai yiwu ɗayanmu ya samar da kyakykyawan alaƙa (tsakaninsa) da Allah maɗaukaki da waliyyansa amma ya barsu a lokacin tsanani ya kasa ganin hanyar tsira daga gare su? Abune sananne babu wani hanyar tsira a lokacin tsanani sai ta hanyar komawa ga Allah maɗaukaki a kowane lokaci. Ayatullah Sayyid Muhammad Taƙi Bahjah (QS).

Magana Mai Hatsari Kuma Mai Girma!

Magana Mai Hatsari Kuma Mai Girma! Babban Ãrifi Sheikh Muhammad Taƙi Bahjah (QS) yace: "Mun kwana tare da mahaifina da wasu abokanmu (a wani guri), amma babu wanda ya tashi sallan asuba sai ni da mahaifina (a cikin mutanen), sai nace wa mahaifina: Me yasa basu tashi salla ba? Sai mahaifina yace: Ya kai ɗana, tsayuwarka a kan hanya madaidaiciya ba ta baka damar yiwa wasu isgili ba, ka da ka dubi mai zunubi da girman kai, domin Allah yana juya zukata yadda ya so, a yayin da Allah ya zaɓe ka a kan hanyar shiriya ba hakan na nuna ka bambanta bane, rahma ce daga gareshi da ta shafeka, tana iya yiwuwa ya cire ta (daga kanka) a ko da yaushe (rahmar), don haka! Ka da ka yi alfahari a aikinka ko a ibadarka, kuma ka guji tunanin cewa: tsayuwa a kan hanya madaidaiciya da ka yi abu ne da ka same shi da kanka, haƙiƙa wannan ƙarfafa ce daga Allah wanda ya keɓance ka da shi... Ya Allah Ka Tabbatar Da Mu A Kan Tafarki Madaidaici. Jama'at Mubarak 25 October 2024, Emran Darussalam.

Astaghfirullah

Istighfaar An ruwaito daga Imam Ja'afar Sadik (AS) daga mahaifinsa daga kakannin sa daga manzon Allah (S) yace: "Albarka ta tabbata ga wanda a ranar ƙiyama ya samu Istigfari (Astaghfirullah) a ƙarƙashin kowane zunubin sa" Masdar: ثواب الأعمال وعقاب الأعمال

Ƙololuwar Rahamar Allah Ga Bayinsa

Ƙololuwar Rahamar Allah Ga Bayinsa. An ruwaito a Hadisul Qudsi cewa Allah (Madaidaicin Sarki) ya ce: “Ma'abota yi mini biyayya suna cikin kulawata, ma'abota gode mini suna cikin ƙarin ni'imata, ma'abota ambatona suna cikin albarkata. Haka nan waɗanda suke saɓa mini ba na cire musu tsammani daga rahamata, Idan suka tuba ni masoyin su ne, idan suka kira ni, ni mai amsawa ne, Idan suka yi rashin lafiya, ni ne likitansu, ina warkar da su ta hanyar jarabawa da fitintinu don in tsarkake su daga zunubai da aibobi." Duba littafin Bihar al-Anwar, juzu'i na 74, shafi na 42. Emran Darussalam  15 November 2024.