Ƙololuwar Rahamar Allah Ga Bayinsa.
An ruwaito a Hadisul Qudsi cewa Allah (Madaidaicin Sarki) ya ce: “Ma'abota yi mini biyayya suna cikin kulawata, ma'abota gode mini suna cikin ƙarin ni'imata, ma'abota ambatona suna cikin albarkata. Haka nan waɗanda suke saɓa mini ba na cire musu tsammani daga rahamata, Idan suka tuba ni masoyin su ne, idan suka kira ni, ni mai amsawa ne, Idan suka yi rashin lafiya, ni ne likitansu, ina warkar da su ta hanyar jarabawa da fitintinu don in tsarkake su daga zunubai da aibobi."
Duba littafin Bihar al-Anwar, juzu'i na 74, shafi na 42.
Emran Darussalam
Comments
Post a Comment