Magana Mai Hatsari Kuma Mai Girma!
Babban Ãrifi Sheikh Muhammad Taƙi Bahjah (QS) yace: "Mun kwana tare da mahaifina da wasu abokanmu (a wani guri), amma babu wanda ya tashi sallan asuba sai ni da mahaifina (a cikin mutanen), sai nace wa mahaifina:
Me yasa basu tashi salla ba? Sai mahaifina yace: Ya kai ɗana, tsayuwarka a kan hanya madaidaiciya ba ta baka damar yiwa wasu isgili ba, ka da ka dubi mai zunubi da girman kai, domin Allah yana juya zukata yadda ya so, a yayin da Allah ya zaɓe ka a kan hanyar shiriya ba hakan na nuna ka bambanta bane, rahma ce daga gareshi da ta shafeka, tana iya yiwuwa ya cire ta (daga kanka) a ko da yaushe (rahmar), don haka! Ka da ka yi alfahari a aikinka ko a ibadarka, kuma ka guji tunanin cewa: tsayuwa a kan hanya madaidaiciya da ka yi abu ne da ka same shi da kanka, haƙiƙa wannan ƙarfafa ce daga Allah wanda ya keɓance ka da shi...
Ya Allah Ka Tabbatar Da Mu A Kan Tafarki Madaidaici.
Jama'at Mubarak
25 October 2024,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment