Skip to main content

Posts

Showing posts from May, 2025

Ya Kai Mai Girma...

Ka Sani, Ya Kai Mai Girma!  Kamar yadda wannan jiki yake da lafiya da rashin lafiya, da magani da waraka, haka nan ruhin ɗan Adam yana da lafiya da cuta, da magani da waraka.   Haƙiƙa Lafiya da amincin ruhi shi ne daidaituwa a kan tafarkin ɗan Adamtaka, Ciwonsa da cutarsa shine gurbacewa da kaucewa tafarkin ɗan Adamtaka, kuma cututtukan ruhi sun fi cututtukan jiki tsanani da hatsari. Saboda waɗancan cututtukan (na jiki) duk tsananin su suna kaiwa lokacin mutuwa suke yayewa.  Da zarar mutuwa ta zo kuma ruhi ya fita daga jiki, to, duk wata cuta ta zahiri da ke kawo rashin daidaito (a jiki) za su gushe, kuma babu wata alaman ciwo a jiki da zai rage, Amma idan (cutan) ya zamto cutane na ruhi - Allah ya kiyaye - to da zarar rai ya bar jiki ya nufi inda aka keɓance masa daga wannan lokacin ciwon (ruhi) zai bayyana. Ya Allah Ka Kiyayemu Daga Cututtukan Ruhi.  ___________________  📓 Arba'una Hadith / Imam Khumaini / shafi na 201 09/05/2024, Emran Darussalam ...

Gareku Muballigai!

Babban Marji'i Sheikh Wahid AlKurasani (DZ) yace: Kada ku cuɗanya maganar ɗan Adam da Maganar Allah. Haƙiƙa wannan Aƙida tuni ne ña jinin Imam Hussain Bin Ali (AS), da ƴayan itacen zalunci da tsare Sayyida Zainab (AS) da akayi, da gadon sare hannun Abulfadlul Abbas... Wajibi ne mu san ƙimar wannan Aƙida mai girma, sannan wajibi ne mu san girman mas'uliyyarmu a kanta (ita aƙidar) A yayin da kuke fita daga gidajenku zuwa tafiya wajen Tabligin Addinin Musulunci, damuwarku ya zamto shine kiyaye rukunan wannan Aƙida, da wannan mazhaba ta gaskiya, idan kuka ga wata zuciya da take da wilaya amma shakka ya tsiro a cikinta, to ku kawar da shakkun (da ke cikinta), idan kuma kuka ga an jefo shubuha, to ku kare ta... A yayin nan ladanku zai zamto fiye da dirhami da dinare! Zai zamto kamar yadda Amirulmu'uminin (AS) yake cewa: "Wanda ya ƙarfafa miskini a cikin addininsa, mai rauni (da'eyfi) iliminsa... Allah zai sanar da shi a yayin da ake sanya shi a cikin ƙabarins...