Ka Sani, Ya Kai Mai Girma!
Kamar yadda wannan jiki yake da lafiya da rashin lafiya, da magani da waraka, haka nan ruhin ɗan Adam yana da lafiya da cuta, da magani da waraka.
Haƙiƙa Lafiya da amincin ruhi shi ne daidaituwa a kan tafarkin ɗan Adamtaka, Ciwonsa da cutarsa shine gurbacewa da kaucewa tafarkin ɗan Adamtaka, kuma cututtukan ruhi sun fi cututtukan jiki tsanani da hatsari.
Saboda waɗancan cututtukan (na jiki) duk tsananin su suna kaiwa lokacin mutuwa suke yayewa.
Da zarar mutuwa ta zo kuma ruhi ya fita daga jiki, to, duk wata cuta ta zahiri da ke kawo rashin daidaito (a jiki) za su gushe, kuma babu wata alaman ciwo a jiki da zai rage, Amma idan (cutan) ya zamto cutane na ruhi - Allah ya kiyaye - to da zarar rai ya bar jiki ya nufi inda aka keɓance masa daga wannan lokacin ciwon (ruhi) zai bayyana.
Ya Allah Ka Kiyayemu Daga Cututtukan Ruhi.
___________________
📓 Arba'una Hadith / Imam Khumaini / shafi na 201
09/05/2024,
Comments
Post a Comment