Babban Marji'i Sheikh Wahid AlKurasani (DZ) yace:
Kada ku cuɗanya maganar ɗan Adam da Maganar Allah.
Haƙiƙa wannan Aƙida tuni ne ña jinin Imam Hussain Bin Ali (AS), da ƴayan itacen zalunci da tsare Sayyida Zainab (AS) da akayi, da gadon sare hannun Abulfadlul Abbas... Wajibi ne mu san ƙimar wannan Aƙida mai girma, sannan wajibi ne mu san girman mas'uliyyarmu a kanta (ita aƙidar)
A yayin da kuke fita daga gidajenku zuwa tafiya wajen Tabligin Addinin Musulunci, damuwarku ya zamto shine kiyaye rukunan wannan Aƙida, da wannan mazhaba ta gaskiya, idan kuka ga wata zuciya da take da wilaya amma shakka ya tsiro a cikinta, to ku kawar da shakkun (da ke cikinta), idan kuma kuka ga an jefo shubuha, to ku kare ta... A yayin nan ladanku zai zamto fiye da dirhami da dinare! Zai zamto kamar yadda Amirulmu'uminin (AS) yake cewa: "Wanda ya ƙarfafa miskini a cikin addininsa, mai rauni (da'eyfi) iliminsa... Allah zai sanar da shi a yayin da ake sanya shi a cikin ƙabarinsa cewa, kace: Allah ne Ubangijina, Muhammad ne Annabina, Ali ne shugabana, Ka'aba ce alƙiblata, Alkur'ani shine farin cikina kuma alƙawarina, Muminai ne ƴan uwa na, Sai Allah yace: haƙiƙa ka zo da hujja, don haka na baka mafificin Aljanna, a yayin ne za'a canza masa ƙabarinsa zuwa raudan Aljanna, daga mafificin raudodinta. (Al'ihtijaj Juz'i na 1 Shafi na 10).
Allah ya yi masa talƙinin kalmar da baya tasawwurin wacce ta fita, wannan kuwa alƙawarin Amirulmu'uminin ne gareku, idan (ku) kuka ƙarfafi aƙida mai rauni domin sanin addininsa, kuka tabbatar da zuciyarsa a kan mazhabi na gaskiya, (zai zamto) farkon tasirin aikin ku a cikin ƙabari shine talƙinin da Allah madaukaki zai yi muku! Sannan tasirin za kai ga ƙabarinsa ya zamto rauda daga raudodin Aljanna.
Haƙiƙa lada ne da ya wuce tsammaninmu, kuma ya fi ƙarfin tasawwurinmu! Ku sanya dukkan ƙoƙarinku a cikin wannan tunani wajen yaɗa girman Ahlulbaiti (AS), kuma nufin ku da hadafinku ya zamto shine yiwa mutane bayanin Alƙur'ani da Sunna kaɗai, kada ku karkata daga wannan khaɗɗin, kuma ku sani! Hanyar yin tasiri a zukatan mutane ya taƙaitu ne da Alƙur'ani da hadisan Itran Annabi (S), hanyar da ba wannan ba kuskure ce! Kada ku cuɗanya maganar ɗan Adam da Maganar Allah, kada ku gwada ƙasa da sama, ko ku yi ƙoƙarin gwada wahami da haƙiƙa.
07/05/2024,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment