Aikin rana shi ne haskakawa ko da tana bayan gajimare ne, haka ma Hujja (Atfs) aikin shi shine shiryarwa ko da yana boyayye ne gare mu a cikin hijabin ɓoyuwa (Gaiba), kamar yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce. Idanunmu ba sa iya ganinsa, amma akwai wani rukuni na jama'a da suka rika ganinsa kuma har yanzu suna ganinsa; kuma ko da ba sa ganinsa (a yanzu) to suna da alaƙa da shi.
Da Alƙalamin Sheikh Imrana Darussalam Azumin Arfa (ranar 9 ga Zul-Hijja) yana da matsayi mai girma a tsarin ibada na Imamiyya (Shi'a), kodayake yana da bambanci kadan da fahimtar Ahlus-Sunna. A mad'hab din Imamiyya, wannan rana tana da daraja ta musamman saboda kasancewarta rana mai tsarki, rana ta addu'a da tuba, kuma rana ce da Allah ke gafartawa bayinsa da dama, musamman ga wadanda ke Arafat da kuma wadanda ba su je Hajji ba. 1. Muhimmancin ranar Arfa a Imamiyya Ranar Arfa ita ce rana ta biyu mafi falala a cikin shekara bayan Laylatul Qadr. Shi’a Imamiyya suna ganin cewa wannan rana ita ce ranar kusanci da Allah, inda ana karanta addu'o'i da yawa, musamman Addu'ar Imamu Husain (a.s) a ranar Arfa da kuma Addu’ar Imam Zainul Abidin (a.s), wadanda suka kunshi falsafa mai zurfi da ruhaniya mai karfi. 2. Azumi a ranar Arfa a Imamiyya Azumin ranar Arfa yana da falala mai girma ga wanda ba ya aikin Hajji, kamar yadda ya zo a hadisan Ahlul Bayt (a.s). Ha...
Comments
Post a Comment