Ayyukan daren farko na watan Rajab:
1– Wanka (Gusl):
An rawaito daga Manzon Allah (SAW) cewa:
“Duk wanda ya samu watan Rajab, ya yi wanka a farkonsa, tsakiyarsa da ƙarshensa, zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.”
2– Raya daren (ibada a daren):
Wannan na daga cikin darare huɗu da ake ƙarfafa mustahabbancin rayar da su.
An rawaito daga Abu Abdullahi (AS), daga mahaifinsa, daga kakansa, daga Ali (AS) cewa ya ce:
“Yana so ya keɓe kansa a darare huɗu cikin shekara: daren farko na Rajab, daren tsakiyar Sha’aban, daren Idin Fitr, da daren Idin layya.”
3– Addu’a lokacin ganin jinjirin wata:
اللّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلّيْنا بالأمْنِ وَالإيْمانِ وَالسَّلامَةِ وَالإسْلامِ رَبِّي وَرَبُّكَ الله عَزَّ وَجَلَّ.
Kuma Manzon Allah (SAW) idan ya ga jinjirin Rajab yana cewa:
اللّهُمَّ بارِكْ لَنا فِي رَجَبٍ وَشَعْبانَ وَبَلِّغْنا شَهْرَ رَمَضانَ وَأَعِنَّا عَلى الصِيامِ وَالقِيامِ وَحِفْظِ اللّسانِ وَغَضِّ البَصَرِ وَلا تَجْعَلْ حَظَّنا مِنْهُ الجُوعَ وَالعَطَشَ.
Salla a daren farko na Rajab:
An rawaito daga Annabi (SAW) cewa:
“Duk wanda ya yi raka’a biyu a daren farko na Rajab bayan sallar Isha’i, yana mai karanta:
Raka’a ta farko:
– Fatiha ɗaya.
– Alam Nashrah ɗaya.
– Qul Huwa Allahu Ahad sau uku.
Raka’a ta biyu:
– Al-Fatiha ɗaya.
– Alam Nashrah ɗaya.
– Qul Huwa Allahu Ahad da Al-Mu’awwidhatain (Falaq da Nas) sau ɗaya ɗaya.
– Ya yi tahiyyah da sallama.
– Ya karanta “La ilaha illallah” sau talatin (30).
– Ya yi salati ga Annabi Muhammad da Ahlul Bait dinsa sau talatin (30).”
Addu'an daren farkon watan Rajab:
اللّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّكَ مَلِكٌ وَأَنَّكَ عَلى كُلِّ شَيٍْ مُقْتَدِرٌ وَأَنَّكَ ما تَشاءُ مِنْ أَمْرٍ يَكُونُ، اللّهُمَّ إِنِّي أَتَوَجَّهُ إِلَيْكَ بِنَبِيِّكَ مُحَمَّدٍ نَبِيِّ الرَّحْمَةِ صَلَّى الله عَلَيْهِ وَآلِهِ يا مُحَمَّدُ يا رَسُولَ الله إِنِّي أَتَوَجَّهُ بِكَ إِلى اللهِ رَبّي ورَبِّكَ لِيُنْجِحَ لي بِكَ طَلِبَتِي، اللّهُمَّ بِنَبِيِّكَ مُحَمَّدٍ وَالاَئِمَّةِ مِنْ أَهْل بَيْتِهِ صَلَّى الله عَلَيْهِ وَعَلَيْهِمْ أَنْجِح طَلِبَتِي (ثم تسأل حاجتك).
21 Dec 2025,
Emran Darussalam.
اللهم صل على محمد وال محمد
ReplyDelete