Uwa Ta Gari
Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam
Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure:
1. Ilimi da Fahimta
> Imam Ali (a.s) yace:
"العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة."
al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm
Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci.
Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta.
2. Ƙauna da Tausayi
> Imam al-Sadiq (a.s) yace:
"رحم الله عبداً أعان ولده على برّه."
al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn
Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).
Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane.
3. Tarbiyya Mai Kyau
Imam Ali (a.s) yace:
"خيرُ ما ورّث الآباءُ الأبناءَ الأدب."
Nahj al-Balāgha, Hikma 399
> Ma’ana: Mafi alherin abin da iyaye ke gadarwa ‘ya’ya shi ne ladabi.
Uwa ta gari tana ɗaukar tarbiyya a matsayin gadon da take barma ƴaƴanta koda bata raye zasu tashi a haka.
4. Haƙuri da Juriyar Rayuwa
> Imam Ali (a.s) yace:
"الصبرُ من الإيمانِ بمنزلةِ الرأسِ من الجسد، ولا إيمان لمن لا صبر له."
Nahj al-Balāgha, al-Hikmah 82
> Ma’ana: Haƙuri ga imani kamar kai ne ga jiki. Babu imani ga wanda babu haƙuri a tare da shi.
Uwa ta gari tana jurewa wahalhalu cikin tawakkali da imani, wannan zaisa ƴaƴanta su taso masu haƙuri da juriya, ta yadda maza daga ƴaƴanta zasu zauna da matansu idan sunyi aure da hakuri, haka mata daga ciki.
5. Tsafta.
Imam al-Sadiq (a.s) yace:
"إن الله يحب الجمال والتجمل، ويكره البؤس والتباؤس."
Wasā’il al-Shīʿa, j.3, bāb nazāfat al-thawb
Ma’ana: Lallai Allah yana son kyau da gyarawa, kuma yana ƙin datti da sakarcin gyara.
Mace ta gari tana gyara gidanta da jikinta da kayan ‘ya’yanta, wannan din Allah na son haka.
6. Kulawa da Aure
Imam al-Sadiq (a.s) yace:
"خيرُ نسائكم التي إذا خلت مع زوجها طرحت له ما يريده منها."
Wasā’il al-Shīʿa, j.14, bāb huqūq al-zawj
Ma’ana: Mafi alherin matayenku ita ce wadda idan ta kasance tare da mijinta, ta kasance masa kamar yadda yake so.
Uwa ta gari kuma matar aure ce ta kwarai, bata mu'amalar aure da wanin mijinta ko sabawa umurnin Allah a fili ko a ɓoye, domin idan ta kasance uwa ballagaza haka ƴaƴan zasu kasance.
7. Sanin Halayyar Yara da Tarbiyyar su
> Imam al-Sadiq (a.s) yace:
"دع ابنك يلعب سبع سنين، ويؤدب سبع سنين، ولازمه سبع سنين، فإن أفلح، وإلا فإنّه من لا خير فيه."
Mustadrak al-Wasā’il, j.2
Ma’ana: Ka bar ɗanka ya yi wasa shekara 7, ka tarbiyyantar da shi shekara 7, sannan ka yi hulɗa da shi shekara 7. Idan ya gyaru, to daidai; idan ba haka ba, to babu alheri a cikinsa.
Wannan ya nuna cewa tarbiyyar uwa dole ne ta zama bisa fahimta da lokaci, ta tsara musu lokacin karatu, lokacin wasa da lokacin bacci, kuma ta kebance lokacin zama da su domin jin halin da suke ciki.
Matar da ta tare waɗannan ita ake kira uwa ta gari, kuma mata ta gari.
Comments
Post a Comment