Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan.
A lokacin da Sayyid Muhammad Baƙir Sadr yake neman ilimi Ƙanwarsa Bintul Hudah tace: "Na kasance tare da ɗan'uwana a wancan lokacin muna tattara kuɗin da muke samu, koda kuwa kaɗan ne, sai Sayyid ya sayi littafi da su, mu karanta mu fahimta. Daga baya sai ya sayar da littafin domin ya sayi wani. Haka muka ci gaba da rayuwa bayan hijirarmu zuwa Najaf al-Ashraf"
- Amma daga ƙarshe mai ya faru? Ilimin shi Sayyid Muhammad Baƙir Sadr (QS) da rubuce rubucen shi sun gajiyar da masu bincike, saboda duk wani mai ilimi da ya karanta littattafansa sai ya jinjina masa, ga kaɗan daga shaidan manyan Malaman Shi'a a kansa:
- Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Abul Qasim Al-Khuʾi (QS) yace:
"Lallai Najaful Ashraf tana alfahari da Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Lallai Allah Maɗaukaki Ya bai wa wannan Sayyid abin da bai ba wa wani ɗalibina ba."
- Sayyid Ruhullah Al-Musawi Al-Khumaini (QS) yace: "Sayyid Muhammad Baqir Sadr yana daga cikin fitattun Mufakkirai na Musulunci. An yi fata cewa Musulunci zai amfana da kasancewarsa fiye da haka. Ina fatan Musulmi za su karanta su kuma nazarci litattafan wannan babban mutum.
- Ayatullah Sayyid Muhammad Rida Al-Musawi Al-Goulbāyagāni (QS) yace: "Lallai Ayatullah Sayyid Sadr, wanda ke da rai kuma madawwami ta ayyukansa masu ɗorewa da manyan hidimominsa a tarihin Musulunci da masana da waɗanda suka sadaukar da rayukansu, ya ƙara samun ɗaukaka da madawwamiya ta hanyar shahadarsa."
- Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Ali Al-Husayni Al-Khamene’i (QS) yace: "Shahidi Sadr yana daga cikin fitattun shaksiyya na musamman a tarihin Musulunci, kuma ana ɗaukan shi a matsayin wata baiwa ta musamman ga duniyar Musulunci. Wanda ya sheƙar da jinin Sadr ba mutum guda ba ne, (zamu iya cewa) dukkan maƙiya Musulunci ne gaba ɗaya."
- Imam Musa al-Sadr (QS) yace:
"Wajibi ne shugaba na siyasa ya dubi yau da gobe da kuma bayan gobe. Wannan kuwa yana nan a cikin Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Kuma abin da ya isa gare shi shi ne cewa ya samu damar samar da mafita ga al'amura da suka kasance masu rikitarwa tsawon shekaru ɗari da hamsin, waɗanda Malamai suka ji tsoron kusantarsu"
Mutumin Da Baya Iya Sayan Littafi A Lokacin Da Yake Neman Ilimi, Daga Ƙarshe Ga Yadda Tasirinshi Ya Buwayi Gabashi Da Yammaci, Dalibin Ilimi Ga Abin Koyinka, Ya Allah Ka Bamu Damar Koyi Dasu.
09/April/2025,
Comments
Post a Comment