Imam Mahdi (Atfs) A Daren Nisfu Sha'aban.
An ruwaito daga Hamza bin Alhassan bin Abdallah bn Abbas bin Ali bin Abidalib (AS) Yace: "Naji Abu Muhammad (AS) yana cewa: Hakika an haifi waliyyin Allah, kuma hujjarsa a kan bayinsa, kuma kalifana a bayana, wanda aka yiwa kaciya a daren Nisfu Sha'aban, a yayin fitowar alfijir, ya kasance farkon wanda yayi masa wanka shine Ridwan mai kula da aljanna, tare da Mala'iku makusanta da ruwan alkausar da salsabil, sannan babata Hakeema bintu Muhammad bin Ali Arrida.
Duba Littafin: Annajmus-saƙeeb Fi Ahwali Imamul Hujja Alga'ib, Juz'i na 1, Shafi na 135.
Allah Ya Maimaita Mana, Ya Sanyamu A Cikin Mukhlisan Masu Jirinsa, Kuma A Cikin Sojojinsa.
26/02/2024,
Comments
Post a Comment