Skip to main content

Daga Kyawawan Dabi'un Imam Aliyu Zainul Abidin (AS)

Daga Kyawawan Dabi'un Imam Aliyu Zainul Abidin (AS)

Imam Zainul Abidin (A.S.) ya kasance yana sa ido da kula kan ayarin mahajjata da ke zuwa daga wurare masu nisa suna ratsa birnin Madina. 
Wata rana ya shiga cikin ɗaya daga cikin ayarin da suka taho, yana mai ce musu yana so ya yi aiki a matsayin bawa mai yi wa mahajjata hidima. A wancan lokaci ana yin tafiya ne a kan dawakai da rakuma, kuma tafiyar tana ɗaukar kwanaki goma ko fiye. A duk wannan lokaci, Imam (A.S.) yana mai da hankali sosai wajen yi wa mahajjata da matafiya hidima, da biya musu bukatu da bin umarninsu.
Wata rana a hanya sai ayarin da Imam yake tare da su suka haɗu da wani da ya san shi. Mutumin ya yi matuƙar mamaki da abin da ya gani, Imami yana hidima wa ayarin mahajjata, sai ya tambayi mutanen ayarin cewa: “Wane ne wannan da kuka taho tare da shi yana yi muku hidima a hanya?”
Sai suka ce: “Hakika ba mu san shi ba; wani kyakkyawan saurayi ne muka haɗu da shi a Madina, ya ba mu kansa don ya yi mana hidima, sai muka yarda muka taho da shi.”
Nan mutumin ya ce: “Da kun san ko wanene shi, da ba ku ɗauke shi a matsayin bawa kuna ba shi umarni da hani ba… domin kuwa shi ne Ali ɗan Husaini ɗan Ali ɗan Abi Talib (A.S.)! Shi ne ɗan Manzon Allah (S)”
A nan ne mutanen ayarin suka garzaya zuwa ga Imam Zainul Abidin (A.S.), suka rusuna suna sumbatar hannuwansa da ƙafafunsa, suna cewa: “Ya ɗan Manzon Allah! Ka roƙa mana Allah kada Ya azabtar da mu a ranar Alƙiyama saboda rashin kunya da munanan ɗabi’unmu a gare ka. Mu ne ya kamata mu yi maka hidima mu kuma bi umarninka.”
Sai Imam (A.S.) ya ce: “Na taɓa gwada haka a baya; duk lokacin da na yi tafiya tare da ayarin da suka san ni, ba sa barina in yi musu hidima. Saboda haka nake son in yi tafiya tare da ayarin da babu wanda ya san ni, domin in sami sa’ar yi wa Musulmi hidima.”

Ya Allah Ka Bamu Ikon Koyi Dasu.

 Ina Tayaku Murnar Zagayowar Ranar Mauludin Imam Ali Zainul Abidin Assajjad (AS). 

24/01/2026,
Emran Darussalam.

Comments

Popular posts from this blog

Daren Nisfu Sha’aban

Daren Nisfu Sha’aban Mai girma da ɗaukaka yana cewa: (Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku da Aljanna wacce fādinta ya kai sammai da ƙasa, wacce aka tanadar wa masu tsoron Allah) Aali Imran: 133. Sheikh Ṣaduq ya rawaito da ingantaccen isnadi daga Hariz as-Sijistani daga Zurara bin A‘yun, ya ce: Na tambayi Abu Ja‘afar (A.S) cewa: Me zaka ce game da daren Nisfu Sha’aban? Sai ya ce: “Allah Maɗaukaki yana gafarta wa halittunsa a wannan daren fiye da adadin gashin awakin ƙabilar Kalbiy, kuma Allah Maɗaukaki yana saukar da mala’ikunSa zuwa saman duniya da kuma ƙasa a Makka.” Kuma an rawaito da isnadi mai inganci daga Hasan bin Faḍḍal, ya ce: Na tambayi Ali bin Musa ar-Riḍa (A.S) game da daren nisfu Sha’aban, sai ya ce: “Dare ne da Allah ke ‘yantar da wuyoyi daga wuta, kuma Yana gafarta manyan zunubai.” Sannan ya ce: “Ku yawaita ambaton Allah Maɗaukaki, da neman gafara da yin addu’a a cikinsa, domin mahaifina (A.S) yana cewa: Addu’a a wannan daren karɓaɓɓiya ce.” Kuma an rawaito daga al-...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan.

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan. A lokacin da Sayyid Muhammad Baƙir Sadr yake neman ilimi Ƙanwarsa Bintul Hudah tace: "Na kasance tare da ɗan'uwana a wancan lokacin muna tattara kuɗin da muke samu, koda kuwa kaɗan ne, sai Sayyid ya sayi littafi da su, mu karanta mu fahimta. Daga baya sai ya sayar da littafin domin ya sayi wani. Haka muka ci gaba da rayuwa bayan hijirarmu zuwa Najaf al-Ashraf" - Amma daga ƙarshe mai ya faru? Ilimin shi Sayyid Muhammad Baƙir Sadr (QS) da rubuce rubucen shi sun gajiyar da masu bincike, saboda duk wani mai ilimi da ya karanta littattafansa sai ya jinjina masa, ga kaɗan daga shaidan manyan Malaman Shi'a a kansa: - Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Abul Qasim Al-Khuʾi (QS) yace: "Lallai Najaful Ashraf tana alfahari da Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Lallai Allah Maɗaukaki Ya bai wa wannan Sayyid abin da bai ba wa wani ɗalibina ba." - Sayyid Ruhullah Al-Musawi Al-Khumaini (QS) yace: "Sayyid Muhammad Baqir Sadr yana daga cikin fitattun M...