A Imanin mu (Mu 'yan shi'a) cewa: Allah mai hikima ne, wannan yasa tun farkon duniya da ya ajiye mutum sai ya sanya kalifan shi a doron kasa, kalifanci shi kuma shine Adam, haka bayan Adam akwai wasiyyin shi Shisu har aka isa kan annabi Nuh haka har zuwa kan manzon Allah ba'ayi wani zamani da babu kalifan Allah a doron kasa ba; har muka iso zuwa wafatin manzo (S) manzo kuma ya kasance tun yana raye baya aiken mutane biyu face sai ya sanya mutum daya a cikin su ya zamo shugaba a tsakanin su, shin kunaga wanda yake yin haka zai bar duniya ba tare da ya sanya mai ci gaba da kula da mutane a bayan shi ba? Sai ya sanya Ali a matsayin wasiyyin shi da umurnin Allah, haka har zuwa kalifofi goma sha biyu a bayan shi har zuwa kan Imam Mahdi (atfs).
Kuma Allah cikin hikimar shi bazai bar qasa haka babu kalifan shi a doron ta ba, sai ya sanya na karshen su wato Imam Mahdi yayi dogon zamani, wanda har yanxu yana raye.
*ABIN DUBAWA*
Idan ya zama a doron kasa babu hujjar Allah to 'Dan adam zai iya zama yana da hujja akan Allah ranar qiyama, misali a yanxu haka da muke rayen nan babu wani Hujjan Allah dake raye, shi 'Dan adam zai sabi Allah ranar kiyama idan ubangiji yace mai yasa ka sabeni zaice ai baka bar Hujjar ka a doron kasa wanda zai zama shi muke komawa gare shi ba, shi kuma Imam Mahdi da zai shiga ghaiba sai ya sanya wasu da ake ce musu marji'ai ya zama ga su ake komawa a zamanin ghaibar Imam, kamar yadda yazo a hadith cewa:
"Wanda ya kasance daga faqihai, mai iya kare kanshi ne, mai iya kiyaye addinin shi, mai 'Da'a wa al'amarin ubangijin shi, to ya zama wajibi ga sauran mutane su bishi".
A wajen 'yan Shi'a Ba'a taba yin wani zamani mai suna zamanin Jahiliyya ba, a kowane zamani 'yan shi'a suna da wanda zasu koma gareshi na abinda ya shafi addinin su, kodai wannan da zasu koma gare shi annabi ne ko kuma wasiyyin annabi ko kuma wanda annabi ya wakilta.
Wannan shine Imanin mu akan Imam Mahdi (atfs).
Allah mun gode maka da ni'imar shi'anci.
Comments
Post a Comment