Skip to main content

AQIDAR SHI'A IMAMIYYA ITHA ASHARIYYA.



Aqeedar Shi'a Imamiyya ta ginu ne akan wadannan abubuwa:

IMANIN MU DA ALLAH.
● Munyi Imani cewa: Sanin Allah (S) wajibi ne akan dukkan Mukallaf da dalilin cewa Allah shike ni'imtawa.
● Allah (S) Samamme ne, ya halacci duniya da dukkan abinda ke cikin ta, haka duk wani abu da ya samu Allah ne ya samar dashi.
● Allah (S) shi ya samar da komai (Baya da buqatar wani ya samar dashi tun farko, kuma bazai kasance babu shi ba anan gaba)
● Allah (S) mai iko ne akan komai, kuma masani ne akan abinda ke fili da abinda ke 'boye.
● Allah (S) mai magana ne (Amma ba magana irin na halittu ba) da dalilin cewa: و كلم الله موسى تكليما
● Allah (S) shi kadai yake bashi da abokin tarayya, hada shi da wani shirka ne.
● Allah (S) ba murakkab bane (Wanda yake a rarrabe) sbd idan da murakkab ne da kenan zai zama yana da buqatan sauran jikin shi, kuma Allah ba mabuqaci bane.
● Allah ba jiki bane, da jiki ne da zai zama akwai buqatar wanda ya halicce shi kenan, kuma Allah shi ya samar da kanshi.
● Baya yiwuwa aga ubangiji, sbd shi ba jiki bane bare ayi amfani da (Sense organs) wajen ganin shi ko taba shi ko jin qamshin shi, kuma abinda ba jiki bane ba yadda za'ayi sense organs ya riske shi.
● Allah  (S) baya kama da kowa kuma baya kama da komai.
● Allah  (S) wadatacce ne, baya buqatar komai a wajen kowa.
● Allah  (S) ba zaune yake a wani waje ba, sbd duk abinda yake a wani waje to zamani da lokaci suna riskar shi, shi kuma ba abinda ke riskar shi, amma yana riskar komai.
● Allah (S) adali ne baya zaluntar kowa.

AQEEDAR MU AKAN ANNABAWA.
● Annabi Muhammad bn Abdullah bn Abdul-Muddalib 'Dan aiken Allah ne, kuma ya isar da sakon ubangiji, kuma mu'ujizozi sun bayyana tare dashi, babban Mu'ujizar shi shine Qur'ani, Al-Qur'ani kuma littafi ne dake bambance tsakanin gsky da qarya, yana nan har zuwa ranar Qiyama. 
● Annabi Muhammad (S) ya kasance annabi ne a qashin kansa tun kafin a aiko shi; bayan hakane aka aiko shi xuwa ga dukkan mutane, domin yace:
كنت نبيا و آدم بين الماء والطين 
Badan haka ba da ya zamto an gabatar da na qasa akan na sama.
● Dukkan Annabawa da Allah ya aiko su mun yadda dasu, kuma dukkan su Ma'asumai ne (Basa sa'bawa ubangiji) Allah ya tsarkake su daga aibu, kuma ya tsarkake su daga mantuwa da ganganci a magana da ayyukan su,daga ranar da aka haife su zuwa ranar komawar su ga mahallici, domin da sun kasance suna aikata zunubi da qimar su zai zube a gurin mutane,sai ya zama hadafin aiko su ya 'baci.
● Munyi imani cewa: Annabi wajibi ne ya zama yana sama da dukkan mutanen shi ta janibin ilimi da sani.
● Annabi Muhammad (S) shine cikamakin annabawa, babu annabi a bayan shi har zuwa ranar qiyama, kamar yadda yazo a Qur'ani:
ما كان محمد أبا أحد من رجالكم ولكن رسول الله و خاتم النبيين
● Isra'i da Mi'iraji da akayi da annabi (S) da jiki akayi a bayyane ba a bacci ba.
● Addinin Musulunci da annabi (S) yazo dashi daga Allah ta share addinan da suka gabata, sbd hukunci da tana canxawa sbd canjin zamani da canjin mutane.

AQEEDAR MU AKAN AHLUL-BAIT (AS)
● Imam Ali (AS) shine shugaba bayan manzon Allah (S) kamar yanda yazo a ruwayar Annabi yana cewa: Ya Ali kai 'Dan uwana ne, kuma mai gadona kaine khalifa a bayana...
● Annabi ke cewa: mamai a bayan Ali (AS) su goma sha 'Daya ne, na farkon su 'Danshi Hassan (AS) sannan Hussain, Sannan Aliyu 'Dan Hussain, sannan Muhammad bn Ali, sannan Ja'afar bn Muhammad Sadiq, sannan Musa bn Ja'afar, sannan Ali bn Musa, sannan Muhammad bn Ali, Sannan Ali bn Muhammad, Sannan Hassan bn Ali, sai khakifa kuma hujjan Allah a doron kasa wato Al'Mahdi (Atfs).
● A Imanin mu wajibi ne Imami ya kasance Ma'asumi (baya sabon Allah)  da ganganci ko da mantuwa, da sun aikata sabon Allah da qimar su ta fadi a wajen mutane, da kenan hikimar saka Imami bayan manzo ya 'baci.
● Wajibi ne Imami ya zama mafi sani a zamanin shi kuma mai shiryar da mutane.
● Munyi Imani da cewa Iyayen Annabin mu Musulmai ne, da yawan su waliayyai ne, Misalin Abu-Dalib mumini ne, irin mu'uminu Ali Fiir'aun (Hizqilu)
● Imam Mahdi (Atfs) shine 'Dan Imam Hassan, an haife shi tun zamanin mahaifin shi, kuma ynxu haka yana Ghaiba yana raye har xuwa ynxu, domin kowane zamani wajibi ne ya kasance akwai hujjar Allah a doron kasa kuma ya kasance wannan hujjan ma'asumi.
● Babu abin mamaki cikin cewa yana raye tun daga wancan zamanin zuwa ynxu, sbd al-ummun da suka gabata wasun suna fin shekara dubu uku a doron kasa, misali Annabi shu'aib da Lookman Isa, Iblis da Dujjal ma har ynxu suna raye, domin shi Allah mai ikone akan komai.
● Ghaiban da Imam Mahdi (Atfs) ya shiga bai shiga dan kanshi ba, ya shiga ne domin umurnin ubangiji. 
● A karshen Duniya Imam mahdi (Atfs) zai bayyana, dalili kuwa shine hadisin Manzo (S) inda yake cewa: Duniya bazata tashi ba har sai wani mutum ya bayyana daga zurriyata, sunan sa irin sunana, Al-kunyarsa irin alkunyata, zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci da danniya.
● Yin umurni da kyakykyawa da hani da mummuna wajibi ne.

~ Wasu abubuwa da ake yadawa idan sukaci karo da wadannan to ba aqeedun mu bane.

~ Daga littafin Al-Firaq wal Mazaahib na Shekh Ja'afar Subhani...Mai Fassara Imrana Haruna Darussalam.

4 April 2019
imrandarussalam99Gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

Muhimmancin Ranar Arfa A Imamiyya.

Da Alƙalamin Sheikh Imrana Darussalam  Azumin Arfa (ranar 9 ga Zul-Hijja) yana da matsayi mai girma a tsarin ibada na Imamiyya (Shi'a), kodayake yana da bambanci kadan da fahimtar Ahlus-Sunna. A mad'hab din Imamiyya, wannan rana tana da daraja ta musamman saboda kasancewarta rana mai tsarki, rana ta addu'a da tuba, kuma rana ce da Allah ke gafartawa bayinsa da dama, musamman ga wadanda ke Arafat da kuma wadanda ba su je Hajji ba. 1. Muhimmancin ranar Arfa a Imamiyya Ranar Arfa ita ce rana ta biyu mafi falala a cikin shekara bayan Laylatul Qadr. Shi’a Imamiyya suna ganin cewa wannan rana ita ce ranar kusanci da Allah, inda ana karanta addu'o'i da yawa, musamman Addu'ar Imamu Husain (a.s) a ranar Arfa da kuma Addu’ar Imam Zainul Abidin (a.s), wadanda suka kunshi falsafa mai zurfi da ruhaniya mai karfi. 2. Azumi a ranar Arfa a Imamiyya Azumin ranar Arfa yana da falala mai girma ga wanda ba ya aikin Hajji, kamar yadda ya zo a hadisan Ahlul Bayt (a.s). Ha...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...

Azumin Ashura Da Tasu'a... Halasci Ko Haramci?

🟥 Haramcin Azumin Ashura Da Tasu’a. 🛑 Matsaya: A mafi yawan ra’ayoyin malamai da ruwayoyin Ahlul Bayt (a.s), azumin ranar Ashura da Tasu’a yana da laifi ko haramci idan: 1. An yi shi da niyyar murna ko farin ciki da abubuwan da suka faru a Karbala. 2. An dauke shi ibada mafi girma ko kamar na Ramadan. 3. An yi shi da nufin koyi da Yazidawa da masu murnar kisan Imam Husain (a.s). 📌 DALILAI NA HARAMCI: 1. 🔥 Dalili na Tarihi: Bayan shahadar Imam Husain (a.s) a ranar Ashura (10 ga Muharram), Gwamnatin Banu Umayyah, musamman Yazid da magoya bayansa, suka mayar da ranar murnar nasara da bukukuwa. An ruwaito cewa: > "Yazid ya bada umarni a dauki wannan rana a matsayin ranar farin ciki da yin ado." Azumin Ashura da ci da sha na musamman (alwala ta musamman, girki, da cin abinci mai dadi) sun samo asali ne daga wannan ƙirƙirar da nufin wanke laifin kisan Husain (a.s). 2. 📚 Dalili daga Riwayoyin Ahlul Bayt (a.s): 📖 Imam Ja’far al-Sadiq (a.s) ya ce: > "Wannan rana (Ashu...