Skip to main content

Falalan Salatin Annabi A Daren Juma'a Da Ranar Ta.

Falalan Salatin Annabi A Daren Juma'a Da Ranar Ta.

Daga Annabi (S) yace: "ku yawaita salati gareni a kowane daren juma'a, wanda daga cikin ku yafi yawaita salati gareni shi zaifi kowa kusanci dani, wanda yayi mini salati ɗari a ranar juma'a zaizo ranar ƙiyama fuskar sa tana haske, wanda kuma yayi min salati dubu a ranar juma'a bazai mutu ba har sai yaga wajen zaman shi a cikin aljanna"

Masdar: Mustadrak Alwasa'el Juz'i 6.

Allahumma salli ala Muhammad wa Ãli Muhammad.

©27/04/2023.
Emran Darussalam.

Comments

Popular posts from this blog

Daren Nisfu Sha’aban

Daren Nisfu Sha’aban Mai girma da ɗaukaka yana cewa: (Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku da Aljanna wacce fādinta ya kai sammai da ƙasa, wacce aka tanadar wa masu tsoron Allah) Aali Imran: 133. Sheikh Ṣaduq ya rawaito da ingantaccen isnadi daga Hariz as-Sijistani daga Zurara bin A‘yun, ya ce: Na tambayi Abu Ja‘afar (A.S) cewa: Me zaka ce game da daren Nisfu Sha’aban? Sai ya ce: “Allah Maɗaukaki yana gafarta wa halittunsa a wannan daren fiye da adadin gashin awakin ƙabilar Kalbiy, kuma Allah Maɗaukaki yana saukar da mala’ikunSa zuwa saman duniya da kuma ƙasa a Makka.” Kuma an rawaito da isnadi mai inganci daga Hasan bin Faḍḍal, ya ce: Na tambayi Ali bin Musa ar-Riḍa (A.S) game da daren nisfu Sha’aban, sai ya ce: “Dare ne da Allah ke ‘yantar da wuyoyi daga wuta, kuma Yana gafarta manyan zunubai.” Sannan ya ce: “Ku yawaita ambaton Allah Maɗaukaki, da neman gafara da yin addu’a a cikinsa, domin mahaifina (A.S) yana cewa: Addu’a a wannan daren karɓaɓɓiya ce.” Kuma an rawaito daga al-...

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan.

Ɗalibin Ilimi Ga Abin Koyi Nan. A lokacin da Sayyid Muhammad Baƙir Sadr yake neman ilimi Ƙanwarsa Bintul Hudah tace: "Na kasance tare da ɗan'uwana a wancan lokacin muna tattara kuɗin da muke samu, koda kuwa kaɗan ne, sai Sayyid ya sayi littafi da su, mu karanta mu fahimta. Daga baya sai ya sayar da littafin domin ya sayi wani. Haka muka ci gaba da rayuwa bayan hijirarmu zuwa Najaf al-Ashraf" - Amma daga ƙarshe mai ya faru? Ilimin shi Sayyid Muhammad Baƙir Sadr (QS) da rubuce rubucen shi sun gajiyar da masu bincike, saboda duk wani mai ilimi da ya karanta littattafansa sai ya jinjina masa, ga kaɗan daga shaidan manyan Malaman Shi'a a kansa: - Ayatullah Al-ʿUzma Sayyid Abul Qasim Al-Khuʾi (QS) yace: "Lallai Najaful Ashraf tana alfahari da Sayyid Muhammad Baqir al-Sadr. Lallai Allah Maɗaukaki Ya bai wa wannan Sayyid abin da bai ba wa wani ɗalibina ba." - Sayyid Ruhullah Al-Musawi Al-Khumaini (QS) yace: "Sayyid Muhammad Baqir Sadr yana daga cikin fitattun M...

AYYUKAN DAREN FARKO NA WATAN RAJAB

Ayyukan daren farko na watan Rajab: 1– Wanka (Gusl): An rawaito daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Duk wanda ya samu watan Rajab, ya yi wanka a farkonsa, tsakiyarsa da ƙarshensa, zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” 2– Raya daren (ibada a daren): Wannan na daga cikin darare huɗu da ake ƙarfafa mustahabbancin rayar da su. An rawaito daga Abu Abdullahi (AS), daga mahaifinsa, daga kakansa, daga Ali (AS) cewa ya ce: “Yana so ya keɓe kansa a darare huɗu cikin shekara: daren farko na Rajab, daren tsakiyar Sha’aban, daren Idin Fitr, da daren Idin layya.” 3– Addu’a lokacin ganin jinjirin wata: اللّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلّيْنا بالأمْنِ وَالإيْمانِ وَالسَّلامَةِ وَالإسْلامِ رَبِّي وَرَبُّكَ الله عَزَّ وَجَلَّ. Kuma Manzon Allah (SAW) idan ya ga jinjirin Rajab yana cewa: اللّهُمَّ بارِكْ لَنا فِي رَجَبٍ وَشَعْبانَ وَبَلِّغْنا شَهْرَ رَمَضانَ وَأَعِنَّا عَلى الصِيامِ وَالقِيامِ وَحِفْظِ اللّسانِ وَغَضِّ البَصَرِ وَلا تَجْعَلْ حَظَّنا مِنْهُ الجُوعَ وَالعَطَشَ. Sal...