Imam Khomeini (QS) yace: "Kada kuce wannan mai rawanin 'barawo ne, abinda ya kamata kuce shine: wannan 'barawon ya sanya rawani" a cikin fadin hakan akwai dalili bayyananne akan cewa shi rawani shi kadai ba zai yuwu a tuhume shi ba, amma qima da mutunci duka yana wajen Malamai, wanda aka yabe su a ruwayoyi dayawa, har yazo a ruwaya cewa: hatta kifaye a cikin ruwa suna nema musu gafara, Matsalar itace: wasu masu neman sai su lissafa kan su a cikin malamai da rawani bayan basu da ilimin.
~ Ya Allah ka kare Malaman mu Rabbaniyyin, ka hanemu cusa kan mu cikin Malamai.
17 APRIL 2020
EMRAN DARUSSALAM
Comments
Post a Comment