Jirgin Tsira! Meka Sani Game Da Jirgin Tsira!
Allah maɗaukakin sarki yana cewa:
وَقَالَ ارْكَبُوا فِيهَا بِسْمِ اللَّهِ مَجْرَاهَا وَمُرْسَاهَا ۚ إِنَّ رَبِّي لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
Me Tafsirul-Amsal yace:
Tsira daga ɗufana baya taɓa yiwuwa ba tare da jirgin tsira (Safinat-Annajati) ba, ba sharaɗi bane sai wannan jirgi ya zamto na katako ko ƙarfe ba, amma me yafi kyau ace wannan jirgi ya zamto addini dake kula da ɗabi'u, kuma ya bada rayuwa Kyakykyawan rayuwa, kuma yayi juriya tare da tsayawa ƙyam a yayin da ruwan ɗufanan karkacewan fikira ya rinƙa tashi sama yana dawowa ƙasa, daga ƙarshe ya isar da mabiyan sa zuwa bakin tafki na Safinat-Annajati.
A bisa wannan ne aka samu ruwayoyi dayawa daga Annabi (S) a littafin shi'a da sunnah dake nuna Ahlul-baitin sa - Imaman shiriya - masu kare addini - cewa sune (Safinatun najati) jirgin tsira nan.
Abu Zaar ya kasance jingine da ɗakin ka'aba yake cewa: "Nine Abuzarr Algiffari, wanda bai sanni ba nine jundub sahabin manzon Allah (S) naji ma'aikin Allah (S) yana cewa: (Misalin Ahlubaiti na misalin jirgin Annabi Nuhu ne, wanda ya hau ya tsira)
A wani ruwayan kuma an ƙara da cewa: (Wanda ya barta ya nutse) ko kuma (wanda ya barta ya halaka).
Wannan hadisi mai girma daga Annabi (S) da saraha yake bayyana mana cewa: a duk sanda ruwan ɗufana na fikiran zamantakewa ko na Aƙida ya ƙwace a tsakanin al'ummar musulmi, tofa hanyar tsira ɗaya tilo itace komawa ga mazhabin Ahlulbaiti (AS), ba komawa mazhabin da mahukuntan da suka gabata suka ƙirƙira ba, wacce bata da wani alaƙa ta kusa kota nesa da Ahlulbaiti (AS).
Kulasar Magana:
Allah maɗaukakin sarki bisa luɗufin sa da ya halicci mutum sai ya sanya masa hanyar tsira, ya aiko Annabawa da manzanni duka domin su nunawa mutum hanyar tsira, wanda idan ya riƙa ya tsira, idan yaƙi ya halaka, to wannan hanya ba komai bace face ruƙo da Alkur'ani da Ahlulbaiti (AS) (Shi yasa Annabi ya kira su da suna jirgin Nuhu, kuma nauyaya biyu) wanda duk yayi ruƙo dasu ya tsira duniya da lahira.
Ya Allah ka tabbatar damu akan yin ruƙo da waɗan nan tsarkaka.
©24/04/2023.
E m r a n D a r u s s a l a m.
Comments
Post a Comment