TAWASSUL DA ƳAR MANZON ALLAH (S).
"Sababin dacewa ta akan rubuta littafin Mafatih Al-jinan ya samu ne don albarkan Sunan Sayyida Fadima Azzahra (AS) mai tsarki.
Sheikh Qommi.
Idan naji ƙunci nakan ɗauki sallaya na ne in hau saman gida sai inyi tawassul da Sayyida Fatima zahra (AS), sai komai ya daidaita.
~ Sayyid Ali Sistani.
Kada ku gafala da muƙamin Sayyida Fatima zahra (AS) mai girma a cikin nafilolin ku na dare.
Sheikh Ãbaadi.
Ina tara dukkanin bukatu na, na tsawon shekara sai in roki Allah a Ayyamul-Fadimiyya, domin ina da yaƙinin Allah zai amsa mini.
~ Sayyid Ali Khamne'i.
Da Sayyida Fatima zahra (AS) Allah yake yin afuwan munanan ayyuka.
~ Sheikh Wahid Alkurasani.
08 November 2022.
© Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment