ZAI FANSHE KA DAGA ABUBUWAN TSORON DAKE CIKIN RAYUWAR BARZAKH.
An hakaito cewa "Wani Malami daga cikin ٓٓArifai yake cewa: "Na kasance ina da Maqoci sai wannan maqoci nawa ya koma ga ubangijin sa, Bayan wasu kwanaki da wafatin sa kwatsam sai na ganshi a mafarki na,Saina tambaye shi cewa ya ka samu kanka a can (Rayuwar barzakh)?
Sai yace dani: ya sayyadi wlh naga Musiba da manya manyan abin tsoro, Masamman lokacin da Mala'iku guda biyu (munkar da nakir) suka zomin, Suka fara min tambayoyi masu yawa, amma ni ban iya amsa musu tambayoyin da suke min ba, sbd na rasa ikon yin magana a daidai wannan lokacin (Harshena ya kasa motsawa na zama kamar kurma) Sai nace a raina:
Niko na shiga uku, wannan wane irin axaba ne mai girma?
Shin ban kasance Mu'umini a rayuwata ba?
Ko ban mutu ina musulmi ba?
Mala'ikun nan suka tsananta akaina da tambayoyi kuma ni na kasa basu amsa, a daidai wannan lokaci kwatsam saiga wani kyakykyawan saurayi ya bayyana, Mai sanye da kanshi, Sai kawai ya shiga tsakanina da wadannan mala'iku guda biyu, Sai ya fara gayamin duk wani amsar tambaya da sukayi min ina amsawa, Sai nace dashi " Rahamar Allah a gareka waye kai"?
Lallai ka ceceni daga azaba mai girma.
Sai Saurayin nan yace: "Ni Mutum ne da aka halitta daga salatin da ka kasance kanayi a rayuwarka ta duniya kana aika wannan salatin ga annabi (S) da iyalan gidansa"
Sai abin ya bani mamaki, nace inama da da yawan salati na gama rayuwata daga farkon ta zuwa karshen ta.
Annabi Muhammad (S) ya kasance yana cewa; "Ku yawaita salati a gareni, domin salatin ku a gareni haske ce a cikin qabarin ku, Kuma haske ce akan siradi yayin tsallakawar ku,kuma haske ce a cikin Aljannah"
قد أفلح من صلّى على محمد و آل محمد.
اللهم صل على محمد و آل محمد
Dan uwan ku Imran Darussalam, Allah yasa mu amfana tare da bamu ikon yawaita salati ga manzo (s) da Ahlul-baiti (AS).
28/April/2018
imrandarussalam99@gmail.com
Comments
Post a Comment