Sheikh Ja'afar Subhani yana daga manya-manyan faƙihai na wannan zamanin, an haife shi a shekarar 1929 miladiyya, shekarar shi 93 a yanzu.
Shi faƙihi ne kuma Malamin usul, kuma mai tafsiri malamin tarihi, kuma malamin Aƙida, kuma failasuf.
Ya fara halartan darasin Marji'in addini Sayyid Hussein burujurdi na fiƙihu da usul tun yana ƙarami, haka nan yana halartan darasin sayyid Muhammad Hujja da Sayyid Ruhullah musawi Khomeini (QS) a hauza ilimiyya a garin Qom, haka nan yayi karatu mai zurfi a wajen Sayyid Muhammad Tabataba'i.
Yadda Manyan malamai suka ce: "Babu wani fage na ilimi face saida ya kutsa cikin sa, yana daga manya-manyan Malaman Shi'a na wannan zamani.
Ya wallafa litattafai dayawa, har zuwa yau yana raye, Allah ya yarda dashi, ya kare shi, ya kuma yawaita masa shekarun sa.
Jaridar Ahlulbaiti Online
Comments
Post a Comment