Fitilar Ƙarshe...
Sayyid Ku'i (QS) a wani muhadarar sa cikin darasi a hauza yake cewa: "misali akwai wani birni da mutanen wannan birni ke rayuwa cikin duhu da hargitsi da karo da juna saboda tsananin duhu, amma kuma sarkin wannan gari mutum ne mai hikima, a binciken sa sai ya gano wata fitila da zata haskaka duka birnin, sai ya kawo wannan fitila ya sanya shi domin mutane su amfana da hasken sa, kowa yayi farin ciki (kan samun wannan fitila), amma bayan wasu ƴan kwanaki sai aka samu wasu suka jefi fitilar suka fasa shi, da yake sarkin garin mutum ne mai son al'ummar sa sai ya kawo wani fitilan daban ya sanya, suka ƙara fasa shi, ya ƙara sanyawa suka fasa, harta kaiga ya sanya fitilu goma sha ɗaya, amma suna fasawa, fitila ɗaya ce ta rage a gurin shi,
Shin ya ya kamata yayi?
Idan ya fito da ragowar wannan fitila mutanen gari zasu ƙara fasa shi su rayu (su) da zuriyar su cikin duhu.
Menene matsayar hikima da hankali a nan?
Hikima da hankali suna cewa: "Rashin sanya wannan fitila da bashi kulawa shine abinda yafi" wannan tasa sarki ya ɓoye fitila ɗaya tilo data rage, da nufin zai jira har zuwa ranar da mutane zasu hankalta su gane muhimmancin wannan fitila su amfana da hasken shi harma su iya bashi kariya.
Kamar hakane Allah ya sanya Imamai masu shiryarwa goma sha biyu, su fitilu ne masu haskaka wa, amma haka mutane suka rinƙa kashe su ɗaya bayan ɗaya, sai Allah ya ɓoye Imami na ƙarshen domin yana ji masa tsoro kuma saboda son da yake yiwa mutane, domin mutane su shiriya dashi, a yayin da zarafi ya bada hakan.
Ya Allah ka gaggauta bayyanar wanda zai haskaka wannan duniya da adalci bayan ta cika da zalunci wato Imam Mahadi (Atfs).
14 May 2023,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment