Daga Imrana Haruna Darussalam
An naƙalto daga Sayyid Ahmad Khomeini (QS) yace: "Jirgin data ɗauko Imam Khomeini (QS) daga faransa zuwa Tehran a lokacin faɗuwan mulkin Sarki Shah, Imam daya sauƙa daga jirgi miliyoyin mutane ne suka tarbe shi, sun taho daga sassa daban-daban suna kiran sunan shi suna murna.
A wannan lokacin ne na waiga naga fuskar Imam (QS), sai naga idanun shi suna zubda ƙwalla, Saina tambaye shi ko meya sashi kuka? bayan wannan lokaci lokacin murna ne da nasara!
Sai ya amsa da cewa: "Ina kuka ne wa Imam Ali (AS)"
Da ya sami irin wannan jama'a a wancan lokaci da ya canza duniya...
~ Ta nan zaka gane zaluncin da aka yiwa Imam Ali (AS).
21/05/2022
© E m r a n D a r u s s a l a m.
Comments
Post a Comment