Skip to main content

Wahabiyanci A Mizani Part ( 1 ).


Wahabiyanci da wanda ya assasashi:
- Ana nasabta firƙan wahabiyya ne ga Muhammad bin Abdulwahab Bn Sulaiman Annajdi, wanda aka haifa a shekarar 1115 Hijiriyya, ya rasu a shekarar 1206 Hijiriyya.

Yayi karatun addini daidai gwargwado, kamar yadda a bayyane yake ya kasance mai yawan bibiya da muɗala'an labaran da suka shafi Musailama al-kazzab, da Sajah, da Aswadul Anasi, da Ɗulaiha Al-asadi, wanda tsatstsauran ra'ayin shi ya fara bayyana tun lokacin da yake karatu, mahaifin sa da wasu daga malaman sa su suka fara yaƙar wannan ra'ayi nashi, suka nuna a nisance shi, inda suke cewa: "Wannan zai ɓata, kuma zai ɓatar da dukkan waɗanda suka nisanci Allah kuma suka kasance shaƙiyyai".

A shekarar 1143 Hijiriyya ya bayyana da'awar sa zuwa ga sabuwar mazhabin sa, amma mahaifin sa da wasu daga malaman sa suka yi ƙoƙarin tsaida shi tare da tunkarar sa, suka karya karsashin kiran nasa, har zuwa lokacin da mahaifinsa ya rasu a shekarar 1153 Hijiriyya, a nanne ya samu damar jaddada da'awar sa tsakanin masu ƙarancin ilimi, da sauran mutane, aka samu dayawa daga cikin su suka bishi, nan mutanen garin suka taso kan shi (saboda yadda suka ga yana ɓatar da mutane) suka yi ƙoƙarin kashe shi, a lokacin ne ya gudu wani gari da ake kira (Uyainah), bayan zuwan shine ya samu kusantar sarkin Uyainah ya auri ƴar uwar sa, ya zauna a nan yana kira zuwa ga kanshi kuma zuwa ga bidi'ar sa, har ta kaiga ya ƙure haƙurin mutanen Uyainah suka kore shi daga garin, haka ya fita zuwa (Addar'iyyah) dake kan hanyar Najid.

Haka fikirar sa ta yaɗu a wannan gari har sarkin garin Muhammad bn Mas'ud ya zama daga mabiyan wannan tafiya tashi da sauran mutane, haka yaci gaba da tasarrufi kamar ma'abocin ijitihadi muɗlaqa, domin kuwa bai kasance yana ɗaukan fatwan magabata (Salaf) ba, kuma baya ɗaukan fatwan faƙihan zamanin sa, dukda a haƙiƙanin gaskiya bayyi karatun da ya kaishi ga ijitihadi ba.

Amma ɗan uwan sa Sheikh Sulaiman bn Abdulwahab ya sifanta shi, wanda shi yafi kowa sanin sa, wanda ya kaiga rubuta littafi guda domin ɓata kiran ɗan uwan shi da tabbatar da hatsarin ta tsakanin al'umma, kamar yadda yazo a wani ibaara inda yake bayyana ta'arifin wahabiyya da wanda ya assasa ta, inda yake cewa: "A yau an jarabci mutane da wanda ke intisaabi zuwa ga kitabu wassunnah, yana istinbaɗi (tsamo hukunce-hukunce) a cikin ta ba tare da ya damu ba, wanda ya saɓa dashi a ra'ayi sunan shi kafuri, wanda kuma a haƙiƙanin gaskiya babu wani alama na ijitihadi data bayyana tare dashi, amma dukda haka ya saye ƙwaƙwalen dayawa daga jahilai, innalillahi wa inna ilaihi raji'un".

Masdar: zaka samu duka wannan da ƙarin bayani a:

- تاريخ نجد لمحمود شكري الآلوسي.
- الصواعق الإلهية في الرد على الوهابية للشيخ سليمان بن عبد الوهاب.
- فتنة الوهابية.

20 May 2022.
Emran Darussalam.

Comments

Popular posts from this blog

Muhimmancin Ranar Arfa A Imamiyya.

Da Alƙalamin Sheikh Imrana Darussalam  Azumin Arfa (ranar 9 ga Zul-Hijja) yana da matsayi mai girma a tsarin ibada na Imamiyya (Shi'a), kodayake yana da bambanci kadan da fahimtar Ahlus-Sunna. A mad'hab din Imamiyya, wannan rana tana da daraja ta musamman saboda kasancewarta rana mai tsarki, rana ta addu'a da tuba, kuma rana ce da Allah ke gafartawa bayinsa da dama, musamman ga wadanda ke Arafat da kuma wadanda ba su je Hajji ba. 1. Muhimmancin ranar Arfa a Imamiyya Ranar Arfa ita ce rana ta biyu mafi falala a cikin shekara bayan Laylatul Qadr. Shi’a Imamiyya suna ganin cewa wannan rana ita ce ranar kusanci da Allah, inda ana karanta addu'o'i da yawa, musamman Addu'ar Imamu Husain (a.s) a ranar Arfa da kuma Addu’ar Imam Zainul Abidin (a.s), wadanda suka kunshi falsafa mai zurfi da ruhaniya mai karfi. 2. Azumi a ranar Arfa a Imamiyya Azumin ranar Arfa yana da falala mai girma ga wanda ba ya aikin Hajji, kamar yadda ya zo a hadisan Ahlul Bayt (a.s). Ha...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...

Azumin Ashura Da Tasu'a... Halasci Ko Haramci?

🟥 Haramcin Azumin Ashura Da Tasu’a. 🛑 Matsaya: A mafi yawan ra’ayoyin malamai da ruwayoyin Ahlul Bayt (a.s), azumin ranar Ashura da Tasu’a yana da laifi ko haramci idan: 1. An yi shi da niyyar murna ko farin ciki da abubuwan da suka faru a Karbala. 2. An dauke shi ibada mafi girma ko kamar na Ramadan. 3. An yi shi da nufin koyi da Yazidawa da masu murnar kisan Imam Husain (a.s). 📌 DALILAI NA HARAMCI: 1. 🔥 Dalili na Tarihi: Bayan shahadar Imam Husain (a.s) a ranar Ashura (10 ga Muharram), Gwamnatin Banu Umayyah, musamman Yazid da magoya bayansa, suka mayar da ranar murnar nasara da bukukuwa. An ruwaito cewa: > "Yazid ya bada umarni a dauki wannan rana a matsayin ranar farin ciki da yin ado." Azumin Ashura da ci da sha na musamman (alwala ta musamman, girki, da cin abinci mai dadi) sun samo asali ne daga wannan ƙirƙirar da nufin wanke laifin kisan Husain (a.s). 2. 📚 Dalili daga Riwayoyin Ahlul Bayt (a.s): 📖 Imam Ja’far al-Sadiq (a.s) ya ce: > "Wannan rana (Ashu...