Usul na fikirar wahabiyya:
- Fikirar wahabiyya tana da usul guda biyu, bayyananne da ɓoyayye.
- Usulin fikirar wahabiyya bayyananne shine: ikhlasi ga tauhidi (Kaɗaitakar Allah), da yaƙar shirka da gumaka.
(Amma a nan gaba zamu tabbatar muku cewa babu wannan a tafiyar ta kusa kota nesa).
- Usulin fikirar wahabiyya ɓoyayye shine: ƙoƙarin keta musulunci da yaɗa fitina da haddasa yaƙi tsakanin musulmi, wannan kam mun ganshi tun farkon assasa wahabiyya zuwa yau... Ta haka muka gane wannan shine asalin fikira da hadafin wahabiyya, an ƙirƙiri wancan na farkon ne domin kauda hankalin masu ƙarancin tunani, abune bayyananne cewa: wannan shi'aar na
( إخلاص التوحيد ومحاربة الشرك)
Shi'ar ne mai jawo hankali da mamaye zuciya, wanda za'a samu jawo hankalin mabiya dayawa kai harda mukhlisai, wanda basu san cewa an sanya wannan Usul na farkon ne domin bayyana na biyu ba, yazo a tarihin wahabiyya cewa: wannan da'awa an tsarata ne tare da assasa ta a asali da umurni kai tsaye daga
وزارة المستعمرين الغربية
Ma'aikatar Turawan Yamma.
Masdar: zaku iya duba:
- أعمدة الإستعمار لخيري حماد.
- تاريخ نجد لسنت جون فيلبي او عبد الله فيلبي.
- مذكرات حاييم وايزمن (أول رئيس وزراء للكيان صحيوني.
- مذكرات مستر همفر.
- الوهابية نقد وتحليل للدكتور همايون همتي.
21 May 2023,
Comments
Post a Comment