Tushen fikirar wahabiyanci:
- Wahabiyya sun kasa Aƙida zuwa kaso biyu:
✓- Na farko: Aƙida wanda yazo daga nassi (Kitabu wassunnah)...Suna ikirarin cewa suna ɗauko shi ne kai tsaye daga kitabu wassunnah (Abin nufi Qur'ani da hadith) ba tare da komawa ijitihadi da Mujitahidai ba, sawa'un waɗan nan Mujitahidai daga sahabbai ne ko tabi'ai ko wasun su daga malaman da suka kaiga marhalan ijitihadi.
✓- Na biyu: Aƙida wanda baizo a nassi ba, sunyi ikirarin cewa: a duk sanda basu samu nassi akan wani abu ba suna komawa ne ga fiƙihun Imam Ahmad bin Hambal da litattafan ibn Taimiyya, amma a haƙiƙanin gaskiya idan muka duba zamu ga akwai tanaƙud cikin raba Aƙidar nan da sukayi zuwa kaso biyu, kuma zamu ga yadda ake samun karo da juna a cikin Aƙidar su, bari mu bada misali kamar haka:
1 - Idan muka duba zamu ga sun daskare akan ma'anar da suka fahimta daga zahirin wasu nassosi, kuma sun saɓawa ƙa'idar usul da ijma'i, don hakane ma Sheikh Muhammad Abdu ya sifanta su da cewa: "Mafi ƙuntatuwa kuma abin kunya a gurin waɗan nan mutane masu makahon taƙlidin shine: (suna ganin wajabcin ɗaukan duk abinda suka fahimce shi a haka daga lafazi da yi masa makauniyar taƙlidi (koda kuwa ya saɓawa shari'a), ba tare da yin waige ga tsarin usul da yake a tsarin addini ba).
~ Zaka samu wannan magana na Sheikh Muhammad Abdu a littafin:
- الإسلام والنصرانية لمحمد عبدة، و هامشة لرشيد رضا: ص 97، الطبعة الثامنة.
2 - Sunce a duk abinda basu samu nassi ba suna komawa ga Imam Ahmad bin Hambal, amma a haƙiƙanin gaskiya sun saɓa da Imam Ahmad bin Hambal wajen kafirta duk musulmin da basu ba, domin kuwa a litattafan Ahmad bin Hambal babu kafirta musulmi, bal akasin hakane a cikin litattafan sa, domin kuwa fatawoyin sa da sirar sa akasin yadda suke ne, kuma baya kafirta musulmi da zunubi ƙarami ko babba, saida barin sallah.
- Zaku iya ƙara tabbatar da haka a littafin sa mai suna:
- العقيدة لأحمد بن حنبل 120.
Amma zamu iya ganin dacewar su da ibn Taimiyya a mafi yawan gurare, domin kuwa yana gaba da duk wanda ya saɓa masa, sannan ya kasance mai raba kan musulmai, ya kasance mai kafirta da nuna fasiƙancin dukkan wanda ya saɓa dashi a masa'il na ijitihadi, sannan ya halasta jinin shi.
- Zamu iya samun wannan a littafin sa mai suna:
- مجموعة فتاوى إبن تيمية 3:349
3 - Haƙiƙa aƙidar wahabiyya a janibin ziyaran maƙabarta wanda ya kamata su fara kafirtawa shine Ahmad bin Hambal, domin kuwa su sun haramta ziyaran ƙabari, harma sun halasta jinin wanda ya ziyarci ƙabari, amma shi kuma Ibn Taimiyya ya naƙalto cewa: Ahmad bin Hambal ya rubuta littafi Juz'i guda akan falalan ziyaran Imam Hussain (AS) a karbala, da abinda ya kamata maziyarci yayi a can, Ibn Taimiyya ɗin yace: Mutane a zamanin Ahmad bin Hambal sun kasance suna ziyartan kabarin sa, tofa wannan shine karo da junan da nake gaya muku a akidar wahabiyya.
Zaka iya duba littafin nan mai suna:
- رأس الحسين لإبن تيمية - المطبوع مع استشهاد الحسين للطبري : 902.
4 - Yana daga Aƙidar wahabiyawa cewa: Wanda ya nemi ceto ko neman taimakon Annabi (S) bayan rasuwar sa yayi babban shirka, domin kuwa sunce bautawa Annabi ne bayan Allah, kuma jini da dukiyar duk wanda yayi haka ya hasta (inji su).
- Zaku iya samun wannan a littafin su mai suna:
- تطهير الإعتقاد للصنعاني : 7
Bayan ya tabbata a sahihan litattafan sunni cewa: Manyan sahabbai da tabi'ai sun kasance suna ziyartan maƙabartu, sun kasance suna neman taimakon Annabi bayan rasuwan shi, kuma Allah yana gaggawan Amsa musu bukatunsu a duk sanda sukayi hakan, duba littafin:
- الزيارة 7 : 101 - 106.
Kuma an naƙalto hakan a litattafai dayawa, kamar baihaƙi, ɗabarani, Ahmad bin Hambal, Ibn Sunni.
Kenan idan muka dauki maganar waɗan nan wahabiyawa zamu ga kenan sahabban nan da tabi'ai duka mushrikai ne, to kenan su dawa suke koyi Annabi? Ahlulbaiti? Sahabbai? Tabi'ai? Ko kuwa sun gina Aƙidar ne akan son rai.
- Ayi haƙuri a wannan karon rubutun yayi tsayi, dalili kuwa idan muka yanke shi ba zamu kaiga natija ba, shi yasa muka tsawaita shi domin mu samu matsaya mai kyau.
22 May 2022,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment