- Wahabiyawa da sauran musulmi (Bidi'ar wahabiyawa mai girma).
- Yana daga Aƙidar wahabiyawa cewa: sunyi imani cewa: su kaɗai ne ma'abota tauhidi tsantsa, amma sauran musulmai waɗanda basu ba mushrikai ne, kuma jinin su da dukiyar su ya halasta, sannan sun halasta a yaƙe su, sannan koda sun furta kalmar nan ta (La'ilaaha illallah Muhammad rasulullah) bata wadatarwa, muddin dai sunyi imani da tabarruki da ƙabarin manzon Allah (S) - suna nufin ziyarar sa da neman ceton sa - shi yasa suke cewa: duk musulmin da yayi imani da ziyaran ƙabari koda na manzon Allah Muhammad (S) ne mushriki ne, kuma shirkan sa tafi na mutanen jahiliyya masu bautan gumaka tsanani.
Zaku samu wannan i'itiƙadi nasu a manyan-manyan litattafan su kamar:
- الرسائل العملية التسع لمحمد بن عبد الوهاب : 79.
- تطهير الإعتقاد للصنعاني : 7، 12 ، 35.
- فتح المجيد : 40 - 41.
- ورسالة أربع القواعد.
- ورسالة كشف الشبهات لمحمد بن عبد الوهاب ، وغيرها ).
- Haka nan idan ka duba shi wannan littafi na كشف الشبهات zaka ga inda Muhammad bn Abdulwahab da kansa yake furta kalmar shirka da mushirkai akan dukkan musulmai (banda mabiyan sa) a guri 24.
- Haka nan a cikin wannan littafi ya kira musulmai da suna kafirai, masu bautan gumaka, masu ridda, marasa tauhidi, kuma maƙiya Allah, masu iddi'a'in musulunci a guri 20.
Tambaya ta anan itace kamar haka: "Shin wannan aƙida ta kafirta dukkan musulmai an samo tane daga magabata (salaf) ko bidi'a ce sabuwa da suka ƙirƙira?
- Ibn Taimiyya dai yana cewa: "Bana kafirta musulmai da zunubin da suka kasance suna aikatawa, koda akan ijitihadi ne sai khawarijh kaɗai.
Duba littafin sa mai suna:
- مجموعة فتاوى إبن تيمية 20:13
Kulasar Rubutun Shin: Su wahabiyawa a wajen su dukkan wani musulmin da basu ba to mushriki ne kafiri, sawa'un yayi imani da ziyaran ƙabarin manzon Allah da neman ceton sa ko bayyi ba, wanda kuwa yayi imani da ziyarar ƙabarin manzon Allah da yin tawassuli dashi to shi bayan ya kafirta jinin shi da dukiyan shi sun halasta a sheƙar dasu.
Duk bawahabiyen da kaga yana zama da kai yana sakar maka fuska, to taƙiyya ce yake yi maka, amma a haƙiƙanin gaskiya ganin tataccen kafuri yake maka, ta yanda da zai samu dama zai iya kashe ka, ya lalata maka dukiyar ka, zaka iya gane haka ta idan kayi wani abu suce maka ɗan bidi'a, ko ɗan gargajiya ba komai hake ke nufi ba face: "wanda bashi da addini" wanda bashi da addini kuma sunan sa...
A janibin yaƙarka da lalata maka dukiya da kwantar da kai su yanka kuwa (Boko haram, ISIS, Taliban) sun ishe ka misali.
23 May 2023,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment