- Wahabiyawa Da Khawarijh.
- Wani abin da zai baka mamaki shine: idan ka duba da kyau zaka ga yadda kamanceceniya yake tsakanin Wahabiyawa da Khawarijawa ta yadda suka karkace daga sauran al'ummar musulmi, ga kaɗan daga inda suke kama:
1 - Khawarijawa sun saɓa da dukkan musulmi inda suke cewa: "Haƙiƙa wanda ya aikata kabira kafiri ne, haka nan wahabiyawa suma sun kafirta duka musulmin da basu ba akan kabira.
Duba littafin:
- كشف الشبهات لمحمد بن عبد الوهاب.
- تطهير الإعتقاد للصنعاني.
2 - Khawarijawa sun fitar da hukuncin cewa: "Dukkan gidan da ake aikata kabaa'ir ya halasta a yaƙi wannan gidan (Ai jinin su ya halasta da dukiyar su, haka Wahabiyawa suka fidda hukunci cewa a yaƙi gidan da ake aikata kabaa'ir, jini da dukiyar su ya halasta a sheƙar dashi.
3 - Wahabiyawa suna kama da Khawarijawa wajen tsanani cikin addini da daskarewa cikin fahimtar addinin, Khawarijawa a yayin da suka karanta fadin Allah cewa: (إن الحكم إلا لله) sai suka ce: wanda ya halasta hukunci haƙiƙa mushriki ne, sai suka ɗau shi'aar ɗin su ta zamo (لا حكم إلا لله) ai babu wani hukunci sai na Allah كلمة حق يراد بها الباطل wannan magana nasu daskarewa ne da jahilci mai girma, a haƙiƙanin gaskiya shi hukunci abune tabbatacce a cikin Alkur'ani mai girma da hadith da siran manzo (S) da Ahlulbaiti (AS) da Sahabbai managarta, Haka nan wahabiyawa a yayin da suka karanta faɗin Allah: (إياك نعبد وإياك نستعين) ai (a gareka muke bauta kuma a gareka muke neman taimako) da ayar nan (من ذا الذي يشفع عنده إلا بإذنه) ai (Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa?) Da ayar nan da yake cewa: (لا يشفعون إلا لمن إرتضى)
Suke cewa: duk wanda ya halasta neman ceto a wajen Annabi (S) da salihai haƙiƙa yayi shirka wa Allah, wanda kuma ya nufi ziyartan Annabi (S) ko kuma ya nemi ceto a gurin shi to haƙiƙa ya riƙi wani Ubangijin daba Allah ba, su kuma shi'aar ɗin su shine:
لا معبود إلا الله، ولا شفاعة إلا لله
Babu abin bautawa sai Allah, Babu ceto sai a gurin Allah.
Wannan shine
كلمة حق يراد بها الباطل.
- Zaku fahimci hakane idan kuka saurari maganar Dr na bauchi Dr. Idris Tanshi, ai a cikin maganar shi cewa yayi ko manzon Allah basa neman taimakon sa, kuma haka haƙiƙanin Aƙidar tasu take, na raina shugaba rasulullah (S).
4 - Ibn Taimiyya yace: "Khawarij sune farkon bidi'a da suka fara bayyana a musulunci, suka kafirta ma'abota musulunci suka halasta jinin su).
- مجموعة فتاوى 20:13.
4 - Hadisan da suka zo kan Khawarijh wasu daga ciki sun ɗabbaƙu akan wahabiyawa...
- Yazo a hadisi cewa: "Daga gabashin ƙasa wasu mutane zasu bayyana, masu karanta Alkur'ani, suna ficewa daga addini kamar yadda kwari yake fita daga cikin baka, wannan itace alamar su"
Yana cikin:
صحيح البخاري - كتاب التوحيد.
Al-ƙisɗalani a sharhin wannan hadisi yake cewa:
(من قبل المشرق أي من جهة شرق المدينة كنجد وما بعدها)
(Ta ɓangaren gabashi ai ta jihhar gabashin madina - kamar najadu da bayan ta).
- Najadu shine matattaran wahabiyawa kuma tushen su na farko wanda daga nan dukka fitinar wahabiyya take fitowa...
Shi yasa malaman zamani sukace: babu buƙatan wallafa littafi domin yin raddi wa wahabiyawa, ya isa ka fito ka bayyana alamomin su, domin su kan su basaso a rinƙa bayyana alamun nasu.
5 - Yazo a hadisi dake sifanta siffofin khawarij cewa: (Suna kashe ma'abota musulunci suyi iddi'a'in cewa ma'abota bautan gumaka ne).
Ibn Taimiyya ma ya kawo a littafin sa.
- Wannan shine sifa da halin wahabiyawa, basa cinna wutar fitina da yaƙi da kisa sai akan ma'abota fuskantar alƙibla, a tarihi babu inda aka kawo tarihin cewa sun yaƙi masu bautan gumaka, kai a cikin littafinsu ma babu tunkarar masu bautan gumaka.
6 - Bukhari ya kawo daga ibn umar a siffanta Khawarijawa cewa: (Haƙiƙa su sun ɗauki wannan ayoyi da ta sauƙa akan kafirai, suka sanya ta akan muminai).
- Duba:
- صحيح البخاري - كتاب إستتابة المرتدين - باب 5)
- A wani ruwayan kuma:, yazo daga Ibn Abbas yace: (Kada ku zamto kamar Khawarijawa, sunyi tawilin ayoyin Alkur'ani akan ma'abota alƙibla, haƙiƙa wannan ayoyi ta sauƙa ne akan Ahlul-kitabi da mushrikai, suka sanya akan su (akan musulmai) suka sheƙar da jini, suka halasta dukiyar su).
Wadannan fa sune wahabiyawa, Ya Allah kayi mana tsari dasu.
24 May 2023,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment