10 GA WATAN RAMADAN; RANAR JUYAYIN TUNAWA DA WAFATIN UMMUL-MUMININ SAYYIDAH KHADIJAH(AS), MATAR ANNABI MUHAMMAD(SAW):
Ummul-Muminin Khadijah bint Khuwailid(as), matar Annabi Muhammad(saw) tayi wafati ne a ranar 10 ga watan Ramadan shekara ta 10 da aiko Annabi(saw), shekara 3 kafin hijira.
Kafin rasuwarta; Khadijah(as) ta ba da gudummawa mai girman gaske wajen kare Annabi(saw) da kuma ci gabantar da Musulunci a lokacin da yake cikin mawuyacin hali. Saboda irin wannan gagarumar gudummawa da Nana Khadijan(as) ta bayar ne; aka ruwaito Manzon Allah(saw) yana cewa:
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻷﻛﺮﻡ(ﺹ): ﻣﺎ ﻗﺎﻡ ﻭﻻ ﺍﺳﺘﻘﺎﻡ ﺩﻳﻨﻲ ﺇﻻ ﺑﺸﻴﺌﻴﻦ: ﻣﺎﻝ ﺧﺪﻳﺠﺔ(ع) ﻭﺳﻴﻒ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻃﺎﻟﺐ(ﻉ) .
(ﺷﺠﺮﺓ ﻃﻮﺑﻰ ﺝ 2 ﺹ 20).
"Ba don dukiyar Khadijah(as) da takobin Ali(as) ba, da wannan addini bai tsaya da kafarsa ba".
(ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﻣﻦ ﺳﻴﺮﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲّ ﺍﻷﻋﻈﻢ 2/121).
Wannan shine ma'anar fadin Allah(t) ga Annabi(saw):
ﻭَﻭَﺟَﺪَﻙَ ﻋَﺎﺋِﻠًﺎ ﻓَﺄَﻏْﻨَﻰ
"Mun sameka marar shi, sai muka wadatar da kai".
(Q:93:8).
Hakan yana nufin, Annabi(saw) ya samu wadata da dukiya mai yawan gaske da yayi amfani da ita wajen yada Musulunci, sabida tarayyarsa Khadijah(as).
Wannan rasuwa ta Khadijah(as) dai ya kasance babban rashi ga Ma'aikin Allah(saw) da kuma 'yarsa Fatima(as) inda har tazo tana kuka tana ce Baban nata(saw) ina mahaifiyata(as), nan take sai Mala'ika Jibril(as) ya sauko ya cewa Annabi(saw):
"Ka ce wa Fatimah(as) cewa Allah(t) ya gina wa mahaifiyarta(as) gida a Al-janna da zinare....".
Saboda irin wannan babban musiba da ta sami Manzon Allah(saw) na wannan rashi na Khadijah(as) da kuma rasuwar baffansa kuma mai kare shi Abu Talib(as), ya sa ya kira wannan shekara (da suka rasu a cikinta) da "Shekarar Bakin Ciki".
Wace Ce Khadijah?
Ita dai Khadijah(as) bint Khuwailid bn Asad bn Abdul Uzza bn Qusay, tana daga cikin manyan matan Kuraishawa kana kuma wacce ta fi su kyau, tun kafin Musulunci ma ana kiranta da suna at-Tahira (tsarkakakkiya) saboda irin kyawawan dabi'unta, kuma ana kiranta da 'Shugaban (matan) Kuraishawa.
Irin wadannan kyawawan halaye nata da kuma irin daukakan da take da shi ya sa wasu daga cikin manyan Kuraishawa, irin su Utbah bn Abi Mu'it, Abu Jahl, Abu Sufyan, da dai sauransu, suka bukaci aurenta da kuma nuna mata kudi, to amma dai taki ta zabi Manzon Allah(saw) saboda halayensa na kwarai da ta gani.
Khadijah(as) mace ce mai dukiya, kana kuma tana son wanda zai kula mata da wannan dukiya ta ta cikin aminci ba tare da cuta ba, don haka sai ta bukaci Manzon Allah(saw), wanda daman tun zamanin Jahiliyya mutanen Makka suna kiransa "As-Sadikul Amin", da ya kula mata da wannan dukiya nata. Da farko dai ya ki yarda, to amma daga baya ya amince da hakan.
Bayan wannan yarda da Manzon Allah(saw) ya yi da wannan bukata ta Khadija(as), sai suka fita kasuwanci tare da wani bawan Khadijan mai suna Maisara. A yayin wannan fatauci dai an sami riba mai yawan gaske, hakan kuwa saboda albarkar da ke tare da Ma'aiki(saw) ne da kuma gaskiyarsa. To bayan dawowarsu, da kuma irin labarin da wannan bawa na Khadijah(as) ya bata dangane da irin kyawawan halaye na Manzon Allah(saw) nan take sai so da kaunarsa ta cika zuciyar Khadijah(as), inda ta bukaci in ya yarda ya aure ta.
Auren Manzon Allah (s) da Khadijah(as):
An ruwaito daga Ammar bn Yasir(r) yana cewa:
"Ni nafi kowa sanin auren Manzon Allah(saw) da Khadijah(as) bint Khuwailid; don na kasance abokin Ma'aiki(saw). Wata rana muna tafiya tare da Manzon Allah(saw) tsakanin Safa da Marwa sai ga Khadijah bint Khuwailid(as) tare da 'yar'uwarta Hala. Lokacin da suka ga Manzon Allah(saw) sai Hala ta ja ni gefe ta ce min: 'Ya Ammar! Abokinka ba shi bukatuwa (da auren) Khadijah? Sai na ce: 'Wallahi ban sani ba. Sai na koma na gaya masa. Sai ya ce min: "Koma ka sa mana lokacin da za mu je mu gana da ita....sai kuwa na koma na aikata hakan (wato muka sa rana). Da ranar ta zo.....sai Manzon Allah (s) ya zo da baffanninsa karkashin jagorancin Abu Talib(as), inda ya karbi aurenta a hannun baffanta Amru bn Asad, kasantuwan mahaifinta, Khuwailid bn Asad ya rasu.
Akwai sabanin masana tarihi akan cewa; Sayyidah Khadijah(as) ta auri Annabi(saw) tana budurwa ko bazawara. Ruwayoyi daga Ahlul-bayt(as) da wasu masana tarihi suna tabbatar da Khadijah(as) ce kadai matar da Annabi(saw) ya aura tana budurwa, amma duk sauran matansa ya aure sune suna zawarawa.
A takaice dai haka auren Manzon Allah(saw) da Khadijah(as) ya kasance.
Matsayin Khadijah A Wajen Manzon Allah(saw):
Bayan gama bukuwan aure, sai Manzon Allah(saw) ya koma gidan Khadijah(as) da zama, wannan gida da ke da dimbin tarihi wajen ci gabantar da musulunci da kuma taimakon marasa galihu.
A yayin zamansu dai, Khadijah(as) ta kasance mace mai tsananin biyayya ga mijinta da kuma taimaka masa a dukkan bangarorin rayuwarsa, kamar yadda shi ma ya kasance hakan tare da ita.
A lokacin da aka aiko shi a matsayin annabi, ita ce mace ta farko da ta fara imani da shi, ta karbi wannan kira nasa, ta ba da dukkan abin da ta mallaka don Allah da kuma ci gabantar da wannan addini.
Babu makawa, dole ne Manzon Allah(saw) ya saka mata saboda irin wannan hidima da ta yi masa da kuma addinin Allah, don haka ya kasance mai tsananin sonta, girmama ta lokacin tana raye da ma bayan rasuwarta(as), daboda matsayin da take da shi a cikin zuciyarsa.
An ruwaito cewa, bayan rasuwarta, a duk lokacin da ya yanka wani abin yanka, ya kan dauki wani bangare na naman ya ce:
"Ku aika wannan wa kawayen Khadijah(as)".
An ce wata rana A'isha bint Abubakar (matar Manzon Allah(saw) ta tambaye shi me yasa yake haka: sai ya ce mata: "Saboda ina sonta".
An ruwaito cewa wata mace ta zo wajen Manzon Allah(saw), a lokacin yana dakin A'isha. Nan take ya tashi ya karbe ta hannu bibbiyu ya gaggauta biya mata bukatan da ta zo nema. Wannan lamari ya ba wa A'isha mamaki, sai ta tambaye shi dalilin hakan, sai ya ce mata: "Ta kasance tana zuwa gurinmu lokacin rayuwar Khadijah(as)".
An ruwaito A'isha tana cewa: 'Wata rana Manzon Allah(saw) zai fita daga gida, sai ya tuna da Khadijah(as), ya fadi wasu kalmomi na girmamawa gare ta. To amma sai na gagara rike kai na sai na ce masa; 'Ita dai ba wani abu ba ne face tsohuwar mace, kuma a halin yanzu Allah ya musanya maka wadanda suka fi ta'. Nan take Manzon Allah(saw) ya mayar mata da martani, cikin fushi yana cewa: "Lallai ba haka ba ne...lalle ban samu wadanda suka fi ta ba. Don kuwa ita ce ta yarda da annabcina a lokacin da kowa ya kyale ni. Ta ba ni dukkan dukiyarta a lokaci mafi tsanani (na bukatuwa da su). Kuma Allah Ya ba ni zuriya ta hannunta, alhali kuwa ya haramta min daga wasunta".
Sayyidah Khadijah(as) ce uwar 'ya'yan Annabi(saw) in kacire Ibrahim Dan Mariya Al-kibdiyya. Kuma Sayyidah Fatimah(as) ita kadai ce mace a 'ya'yan Annabi(saw) da kuma Khadijah(as), kamar yanda hadisai daga Ahlul-bayt(as) suka tabbatar.
Barka gare ki Ya Khadijah(as), barka gare ki Ya ke wacce Allah Ya ke sonki kuma Ya kuma miki alkawarin dawwama cikin ni'iman Al-jannah.
An ruwaito cewa Mala'ika Jibril(as) ya zo wajen Manzon Allah (s) ya ce masa; "Ya Rasulallah! Ga Khadijah(as) nan za ta zo gurinka da kwaryar abinci, idan ta zo ka isar da gaisuwar Ubangijinta gare ta da kuma tawa gaisuwar, ka kuma yi mata bushara da gida a Aljanna da aka gina shi da zinare....."
A saboda haka ne Manzon Allah(saw) ya ce:
"Mafiya daukakan matan Al-jannah su ne: Khadijah bint Khuwailid(as), Fatima bint Muhammad(as), Maryam bint Imran(as), Asiya bint Muzahim(as), (matar Fir'auna).
Don karin bayani, duba:
ﺍﺑﻦ ﻛﺜﻴﺮ، ﺍﻟﺒﺪﺍﻳﺔ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﻳﺔ، ﺝ 2 ، ﺹ .293
ﺍﺑﻦ ﺳﻴﺪ ﺍﻟﻨﺎﺱ، ﻋﻴﻮﻥ ﺍﻻﺛﺮﻓﻲ ﻓﻨﻮﻥ ﺍﻟﻤﻐﺎﺯﻱ ﻭﺍﻟﺸﻤﺎﺋﻞ ﻭﺍﻟﺴﻴﺮ، ﺝ 1 ، ﺹ .63
ﺍﺑﻦ ﺍﺛﻴﺮ ﺍﻟﺠﺰﺭﻱ، ﺃﺳﺪ ﺍﻟﻐﺎﺑﺔ ﻓﻲ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ، ﺝ 1 ، ﺹ .23
ﺍﺑﻦ ﺳﻌﺪ، ﺍﻟﻄﺒﻘﺎﺕ ﺍﻟﻜﺒﺮﻯ، ﺝ 8 ، ﺹ 174
ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﺒﺮ، ﺍﻻﺳﺘﻴﻌﺎﺏ، ﺝ 4 ، ﺹ .1817
ﺍﻟﻤﺠﻠﺴﻲ، ﺑﺤﺎﺭﺍﻷﻧﻮﺍﺭ، ﺝ 100 ، ﺹ .189
ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ، ﺗﺬﻛﺮﺓ ﺍﻟﺨﻮﺍﺹ، ﺝ 2 ، ﺹ .300
ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺒﺮ، ﺍﻻﺳﺘﻴﻌﺎﺏ، ﺝ 4 ، ﺹ .1824.
ﺍﻟﻤﺴﻌﻮﺩﻱ، ﻣﺮﻭﺝ ﺍﻟﺬﻫﺐ، ﺝ 2 ، ﺹ 282.
ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ، ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻻﻣﻢ ﻭﺍﻟﻤﻠﻮﻙ، ﺝ 11 ، ﺹ :493.
➖➖➖➖➖➖➖➖➖
Abdulrahman Murtala - 07063758368
🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹
Comments
Post a Comment