Sayyid Ali Bahbahani ya nakalto daga daga dalibin Sheikh Murtada Ansari (R) cewa: "Na tafi Najaf domin kammala karatuna na addini, saina samu halartan darasin da Sheikh Murtada Ansari yake gabatarwa, saidai a wannan lokaci naji bana fahimtar darasin yadda yakamata, naji bakin ciki matuka da wannan hali dana tsinci kaina (Na rashin fahimtar karatu) daga karshe dai haka nayi tawassuli da Amirul-muminin Imam Ali Amincin Allah su kara tabbata a gareshi, a daren wannan rana ne nayi mafarki da Imam Ali (AS) har ya karanta min " Bismillahir rahmanir rahim," a kunne na, wayewan gari keda wuya na halarci wajen darasi karo na biyu sai naji ina fahimtar darasin yadda ya kamata, ta kaiga nakanyi tambaya tare da bijiro da mas'aloli wa Sheikh, watarana muna sauraron darasin Sheikh sai ya zamto nayi magana dayawa a yayin darasin, sannan na bijiro da mas'aloli ina fada Sheikh Murtada yana karewa, bayan mun kammala darasi sai Sheikh din ya matso kusa dani, ya kawo bakin sa kusa da kunnena ya cemin: "Wannan da ya karanta maka bismillahir rahmanir rahim" a kunnen ka, haka nima ya karanta min a kunnena har zuwa waladdaallin" Nan fa nayi mamakin wannan al'amari, domin ni ban taba gayawa kowa mafarkin da nayi ba, Anan ne na gane cewa shi Sheikh Murtada Ansari yana da wani mukami da girma na musamman a wajen Imaman shiriya, nan na sallama masa dukkan sallamawa.
Allah ka yiwa Sheikh Murtada Ansari rahama, ka jikan malaman mu da suka rigamu gidan gaskiya.
© 27 DECEMBER 2021
© Emran Darussalam
© imrandarussalam99@gmail.com
Comments
Post a Comment