Skip to main content

DAGA TASKAR MAGABATA (3)



Shaheed Mutahhari (R) ya naqalto daga Malamin sa masanin Allah wato Mirza Ali Shirazi yake cewa:

"A cikin mafarki na naga cewa gani nan na mutu, a lokacin ne naga ruhi na yabar jiki na, nan fa naga an dauke ni zuwa makabarta, bayan an kaini aka binne ni, haka suka barni ni kadai cikin kabari ina tsoro, kwatsam sai naga kare yana kokarin shigowa cikin kabari na, sai nayi tunanin wannan wani mummunan aiki ne na aikata shi ya fito min a suffar kare, haka nan na shiga damuwa, a wannan lokacin ne Sayyidush-shuhada Imam Hussein (AS) yazo min yace: Kada ka damu domin zan nisantar dashi daga gareka"

Daga littafin:
 قصص من عالم الأرواح.
Shafi na 51.

Haka ke nuna Imam Hussein (AS) baya barin wanda yayi ruqo dashi anan duniya.

#السلام_عليك_يا_أبا_عبدالله.

© 17/2/2022
© Emran Darussalam

Comments

Popular posts from this blog

Daren Nisfu Sha’aban

Daren Nisfu Sha’aban Mai girma da ɗaukaka yana cewa: (Ku yi gaggawa zuwa ga gafarar Ubangijinku da Aljanna wacce fādinta ya kai sammai da ƙasa, wacce aka tanadar wa masu tsoron Allah) Aali Imran: 133. Sheikh Ṣaduq ya rawaito da ingantaccen isnadi daga Hariz as-Sijistani daga Zurara bin A‘yun, ya ce: Na tambayi Abu Ja‘afar (A.S) cewa: Me zaka ce game da daren Nisfu Sha’aban? Sai ya ce: “Allah Maɗaukaki yana gafarta wa halittunsa a wannan daren fiye da adadin gashin awakin ƙabilar Kalbiy, kuma Allah Maɗaukaki yana saukar da mala’ikunSa zuwa saman duniya da kuma ƙasa a Makka.” Kuma an rawaito da isnadi mai inganci daga Hasan bin Faḍḍal, ya ce: Na tambayi Ali bin Musa ar-Riḍa (A.S) game da daren nisfu Sha’aban, sai ya ce: “Dare ne da Allah ke ‘yantar da wuyoyi daga wuta, kuma Yana gafarta manyan zunubai.” Sannan ya ce: “Ku yawaita ambaton Allah Maɗaukaki, da neman gafara da yin addu’a a cikinsa, domin mahaifina (A.S) yana cewa: Addu’a a wannan daren karɓaɓɓiya ce.” Kuma an rawaito daga al-...

UWA TA GARI...

Uwa Ta Gari Da Alƙalamin Sheikh Imrana Haruna Darussalam  Uwa ta gari itace wacce ta tanadi waɗannan abubuwa kafin tayi aure: 1. Ilimi da Fahimta > Imam Ali (a.s) yace: "العلمُ ميراثُ الأنبياء، والمالُ ميراثُ الفراعنة." al-Kāfī, j.1, bāb fadl al-ʿilm  Ma’ana: Ilimi gadon annabawa ne, dukiya kuwa gadon masu zalunci. Wannan yana nuna cewa mace ta gari na buƙatar ilimi don tarbiyyar ƴayanta, domin kuwa itace Malama ta farko da ke fara bada ilimi a yaro tun a tsumman goyo kafin a kaiga kaishi makaranta. 2. Ƙauna da Tausayi > Imam al-Sadiq (a.s) yace: "رحم الله عبداً أعان ولده على برّه." al-Kāfī, j.6, bāb birr al-wālidayn  Ma’ana: Allah ya ji ƙan bawan da ya taimaka wa ɗansa wajen yi masa biyayya (ta hanyar ƙauna da kulawa).  Uwa ta gari tana cika gida da ƙauna da tausayi, a yayin da uwa ta haɗe wadannan abubuwa biyu to zaka samu ɗanta ya taso da tausayin al'umma da son mutane, hakan zaisa ya zamto abin so wajen mutane. 3. Tarbiyya Mai Kyau Imam Ali...

AYYUKAN DAREN FARKO NA WATAN RAJAB

Ayyukan daren farko na watan Rajab: 1– Wanka (Gusl): An rawaito daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Duk wanda ya samu watan Rajab, ya yi wanka a farkonsa, tsakiyarsa da ƙarshensa, zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” 2– Raya daren (ibada a daren): Wannan na daga cikin darare huɗu da ake ƙarfafa mustahabbancin rayar da su. An rawaito daga Abu Abdullahi (AS), daga mahaifinsa, daga kakansa, daga Ali (AS) cewa ya ce: “Yana so ya keɓe kansa a darare huɗu cikin shekara: daren farko na Rajab, daren tsakiyar Sha’aban, daren Idin Fitr, da daren Idin layya.” 3– Addu’a lokacin ganin jinjirin wata: اللّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلّيْنا بالأمْنِ وَالإيْمانِ وَالسَّلامَةِ وَالإسْلامِ رَبِّي وَرَبُّكَ الله عَزَّ وَجَلَّ. Kuma Manzon Allah (SAW) idan ya ga jinjirin Rajab yana cewa: اللّهُمَّ بارِكْ لَنا فِي رَجَبٍ وَشَعْبانَ وَبَلِّغْنا شَهْرَ رَمَضانَ وَأَعِنَّا عَلى الصِيامِ وَالقِيامِ وَحِفْظِ اللّسانِ وَغَضِّ البَصَرِ وَلا تَجْعَلْ حَظَّنا مِنْهُ الجُوعَ وَالعَطَشَ. Sal...