Babban Malamin nan na shi'a wato Sayyid Abdul-A'alah sabzawaari (R) ya kasance yana cewa: "Idan aka goge isnadi da sunan Imamin da aka ruwaito hadisi daga gare shi, kuma aka karanta min yadda matanin hadisin yake, zan iya cewa: Wannan matanin hadisin ya fito ne daga Imami ma'asumi waane (Allah ya qara masa yarda)...
Yazo cewa: wataran wani malami ya samo shi, sai ya kawo wani hadisi ya nasabta hadisin zuwa ga Imam Muhammad Baqeer (AS) Sai Sayyid Abdul-A'alah yace masa: Wannan hadisi daka kawo banji kamshin Imam Muhammad Baqeer (AS) a cikin sa ba, kamshin da naji na Imam Ja'afar Sadiq (AS) ne, take aka dauko littafi domin a duba, da aka duba sai aka samu hadisin daga Imam Ja'afar Sadiq (AS) kamar yadda ya gaya musu.
Shi yasa ake yawan magana akan shi cewa: A zamanin shi ba'a sami wanda yayi kusa dashi wajen haddace ruwayoyi da isnadi ba, yana da cikakkiyar sani akan abinda ya shafi ilimin hadisi, ta yanda idan ka karanta masa hadisi ba tare da ka nasabtata zuwa wani Imami ba zaice maka, wannan harshen Imami waane ne, wannan Kuma na Imami waane, sbd yawaita bibiya da karanta da haddan Hadisai.
______________
15/5/2022
© E m r a n D a r u s s a l a m.
Comments
Post a Comment