Sayyid Ku'i (R) a wani muhadaran da ya gabatar a Hauza yake cewa: "Misali: akwai wani birni da cikin sa akwai wasu mutane dake rayuwa cikin duhu mai tsanani, matsaloli kuma suna faruwa dalilin wannan duhun da suke ciki, sarkin garin kuma ya kasance mutum ne mai hikima, sai a binciken sa ya gano fitila da zata iya haskaka garin dukkan shi, sai wannan sarki ya sanya wannan fitila domin mutane su amfana gaba daya, Haka mutane suka yi farin ciki da hakan, bayan wani ɗan lokaci sai aka samu wasu daga mutanen garin suka fasa fitilar, amma da yake shi wannan sarki yana son mutanen sa sai ya sanya wata fitilar daban, sai suka ƙara fasawa, haka ya rinka sanyawa suna fasawa har suka fasa fitilu goma sha daya, sai ya zamto fitila ɗaya tilo ta rage masa, ko yaya zayyi?
Idan ya fitar da fitila ta goma shs biyun zasu ƙara fasawa.
Hikima da hankali abinda suke cewa anan shine: Kula da wannan fitila shine yafi.
Sai wannan sarki ya boye fitilar, yaƙi fitar dashi.
Yayi hakane domin mutanen su hankalta kuma su san muhimmancin wannan fitila, ta yanda babu wani da zai ƙara yunkurin fasawa, idan wannan lokaci yayi sannan ya fidda shi.
ABIN LURA
Kamar hakane Allah maɗaukaki ya sanya mana Imamai goma sha biyu a bayan fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S), su ɗin fitilu ne masu haske dake haskaka ma mutane hanya, (su shiryar dasu) amma sai mutane suka kashe su ɗaya bayan ɗaya, wannan dalili yasa Allah madaukaki ya ɓoye na Karshen su Imam Mahdi (Atfs) saboda son da yake wa mutane, sai su amfana da shi a yayin da suka shirya, kuma suka hankalta suka bukaci hakan, a lokacin ne duniya zata cika da zalunci sai mutane su gane cewa babu mafita sai ta hanyar wannan fitila (Imam Mahdi (Atfs), sai ya bayyana ya cika kasa da adalci, bayan ta cika da zalunci.
Ya Allah ka gaggauta bayyanar Imam Mahdi (Atfs)
09-07-2022.
© Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment