A Sa'oin Ƙarshe Na Rayuwar Ka Me Kake Ga Shi Zaka Aikata Domin Ya zamto Aikin Ka Na Ƙarshe A Wannan Duniya.
Sheikh Ãdil Ãli Jauhar yace: "Wani daga ɗaliban Sayyid Mahdi Shirazi (R) ya naƙalto cewa: Watarana kafin fara darasi na samu Sayyid nace masa: "Ina da tambaya da nake bukatar amsar ta, ina fatan zaku bani lokacin ku, sannan ina neman uzuri idan amsar wannan tambaya tawa ta zamto ba muhimmiya ba a gurin ku.
Sai Sayyid yace: Tafaddal, yi tambayar ka.
Sai nace: Misali Sayyid kasan cewa zaka bar duniya nan da awa guda ko kwana ɗaya, me zaka aikata a iya waɗannan lokuta da suka rage maka a rayuwa, sannan wane aiki ne zaka yi saurin aikata shi?
Sai sayyid ya amsa min cikin sauri ba tare da jinkiri ba (a al'adar Sayyid ya kasance idan akayi masa tambaya sai ya ɗan ɗau lokaci kafin ya bada amsa), amma a wannan lokaci babu jinkiri sai ya amsa da cewa: "Bazan aikata wani aiki ba sai wannan da nake yi yanzu" (ya kasance a lokacin yana muɗali'an litattafin jawahir ne, yana kintsa kan sa kafin shiga aji), wannan lokaci - kamar yadda mukace - kusan fara darasi ne.
Kawai wannan shine zai kasance mafificin aiki ga Marji'an taƙlidi, ina nufin muɗali'an hukunce-hukuncen shari'a, da koyar da ɗalibai, wannan shine muhimmin wajibin da ya hau kansu.
~ Ya Allah kasa muyi kyakykyawan ƙarshe ~
© 15-01-2023.
Comments
Post a Comment