Hujjatul Islam Sheikh Nur Dass (H) Malami ne na shi'a, kuma wakilin Babban Marji'i Ayatullah Sayyid Ali Khamnei (DZ) bangaren Shari'a a Najeriya, wakilcin da ba'a taɓa samun irin sa ba a kaf Nahiyar Afrika.
Yana daga cikin ƙoƙarin shi a Najeriya:
Assasa Mu'assasar RASULUL A'AZAM FOUNDATION (RAAF), wacce ta kasance mu'assasa ce ta Shi'a Zallah tare da yima wannan Mu'assasar rijista a hukuman ce, ta cika sharruɗa dukkan sharruɗa.
Rasulul A'azam Foundation (RAAF) Mu'assasa ce dake buɗe makarantun Hauzozin ilimi da markazozi dan yada addinin musulunci cikin shi'anci tsantsa, tana da Makarantun Hauzozi da Masallatai a jihohi daban daban a faɗin Nigeria, kuma duka makarantu ne masu rijista waɗanda aka gina akan tsari, kuma makarantu ne da aka yi musu ginin zamani.
Tana da keɓantaccen sashe na abinda ya shafi kira da tabligh, wannan sashe ya tara muballigai (Masu isar da sakon musulunci) da yawa a karkashin sa, duka dan Isar da sakon Ahlul-bayt (AS) a faɗin kasar ta Nigeria, Shugaban wannan sashe shine Hujjatul Islam wal muslimin Shekh Bashir lawal kano (H), wanda ake masa laqabi da Sautush~shi'a.
Haka nan wannan shugaba kuma wakilin Sayyed Ali Khamnei (DZ) ya assasa babban Hauza a birnin kano, sunan wannan Makaranta HAUZATU BAQIRUL ULUM, wanda shi ke jagorantar wannan makaranta, an samu ɗalibai dayawa wadanda suka sha madarar ilimi suka fita suma Suna taimakawa a ɓangaren tabligh yanzu haka.
Ta ɓangaren ƙoƙari da yayi a ɓangaren siyasa da janibin jama'a kuma akwai:
1. Yaɗa abinda ya shafi saƙafa da siyasa tsakanin jama'a, yayi haka ne domin farkar da ƴan shi'ar ƙasar wajen shiga cikin al'amuran da suka shafi ƙasa, kuma ayi dasu saboda suma ƴan ƙasa ne masu lasisi.
2. Wayar da kan ƴa shi'a a abinda ya shafi mahimmancin siyasa, da tsayawa takara (kamar sauran ƴan ƙasa da sauran ƙungiyoyi).
3. ƙoƙarin shi na samar da haɗin kai tsakanin ƙungiyoyin Musulunci (SHI'A DA SUNNA) da ƴan shi'a suma a junan su (bil akhas), haƙiƙa ya taka rawar gani a waɗan nan janibobin.
4. Gusar da mummunan ganin da hukuma take yiwa ƴan shi'a daga ƴan tawaye kuma masu taka doka da oda, zuwa ƴan ƙasa na gari masu kishin ƙasar su.
5. Akwai kuma ƙoƙarin shi na tarwatsa shirin wahabiyawa da suke na ƙoƙarin ɓata sunan shi'anci a cikin ƙasa, tare da sauran matakai da suka dace ta ɓangaren hukuma, kuma Alhmdlh ya samu nasara sosai a wannan yunƙuri nashi.
6. Karantar da aƙidar shi'anci yadda yake asali a musulunci, tatacce tsaftatacce daga ruwayoyin da wahabiyawa suke kawowa na ƙarya, tare da nisantar dashi daga kaucewa tsari.
6. Wannan Mu'assasa ta RASULUL A'AZAM FOUNDATION (RAAF) ta gina Masallacin Shi'a na Juma'a wanda shine farkon masallacin Shi'a a kaf Nigeria, sannan an gina shi bisa tsari da Neman izinin hukuma, wanda aka gina a Dawanau dawakin tofa dake kano Nigeria, Masallaci ne babba wanda a gefen shi aka Gina ajujuwa dan karantarwa da babban ɗakin taro wato (Hall) da banɗakai duka domin ciyar da shi'anci gaba, Akan gabatar da salloli biyar na yau da kullum a cikin sa, da sauran ibadoji da tarurrukan addini.
7. Tura adadi mai yawa na ɗalibai makarantun Hauza domin ci gaba da karatun su na addini da samun ilimi mai zurfi.
8. Ya taimaka wajen ƙarfafawa matasa da taimaka musu domin ci gaba da Karatun jami'a, kuma Alhamdulillah dayawa sun amfana da wannan abin alkairin, haka har yanxu wasu Suna amfana.
9. Yana Daga abun da yayi: kiran shi da yayita yi tsakanin hukumar Nigeria da Harkar Musulunci a Nigeria wanda Sheikh Zakzaki ke jagoranta dan zama a tattauna a gane ina Matsala take tare da magance ta ya zama daga ƙarshe an samu fahimtar juna a tsakani.
10. Bai tsaya nan ba a ɓangaren hidimtawa addini duk dare idan ka kira wayar shi zai amsa, koka tura masa sakon tex na abinda ya shafi tambaya ko neman warware wani ishkali da ya bijiro maka zai amsa maka, kodai ta hanyar message ko ta hanyar kira.
Duka kuma tare da taimakawan Sauran malaman dake tare da shi, Sheikh Saleh Muhammad Sani Zaria da Sheikh Bashir Lawal kano, da sauran Malamai a Hauza matattarar alkairai.
Fatan mu shine: Allah ya kare shi, tare da bashi ƙarfin gwiwa cikin abubuwan da yake gabatarwa, Allah ka kare su.
Jaridar Ahlulbaiti Online
Comments
Post a Comment