Manzon Allah (S) ya ce: "Wanda ya wulakanta wani muminin namiji ko mace, ko ya raina shi saboda talaucinsa ko rashin abin hannunsa, Allah Madaukaki zai tona asirinsa a ranar Alƙiyama sannan ya kunyata shi." ¹
A wani faɗin (mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce: "Ku sani, wanda ya raina wani miskini Musulmi, to haƙiƙa ya yi sako-sako da hakkin Allah ne, kuma Allah zai yi sako-sako da shi a ranar Alƙiyama, sai dai idan ya tuba." Kuma ya ce (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa): "Wanda ya girmama miskini Musulmi, zai haɗu da Allah a ranar Alƙiyama alhali yana mai yarda da shi." ²
Ha'ilau an ruwaito daga Imam Ja'afar Sadiq (AS) yace: "Wanda ya haɗu da faƙiri musulmi (talaka ), ya yi masa sallama saɓanin yadda yake yi wa mai arziki sallama, zai haɗu da Allah Madaukaki a ranar Alƙiyama alhali Allah yana mai fushi da shi" ³
1 - Bihar Al-anwar, Juz'i na 44 Shafi na 52.
2 - Bihar Al-anwar Juz'i na 01, Shafi na 212.
3 - Duba Littafin Amāli Saduq, Juz'i na 5 Shafi na 359.
Ya Allah Ka Wadatamu Da Wadatarka, Ka Kiyayemu Ɓatanci Ko Wulaƙanta Dukkan Halittunka.
02 November 2024,
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment