"Wanda ke kula da tururuwa a cikin duhu rami...
Kana tsammani ko tunanin wata rana ya manta da kai...
Ka ji da yaƙini cewa a ko da yaushe yana sane da kai, kuma yana jiran ka kira shi ya amsa maka, ka roƙe shi ya biya maka buƙatu.
Mafificin lokacin amsa kiran bayi da biya musu buƙatu shine dare, a sanda idanu suka yi bacci, shi ko a lokacin ya ke shela cewa: "Wa ke da buƙatu a cikin bayina"!!!
Ya Allah ka yi mana abinda ya ke shine alkairi a gurinka, ka tabbatar da mu cikin yi maka ɗa'a.
04/05/2024,
Emran Darussalam
Comments
Post a Comment