Hassan ya kasance ɗan shi'a kuma dalibi a makarantar da mafi yawan ɗaliban ta Ahlussunnah ne.
Wata rana malami zai fita daga aji sai yace:
Ya kai Hassan taso ka zauna a gurin zama na, kada ka yarda da wani rikici ko suruce-suruce a tsakanin ɗalibai har zuwa dawowa na!.
Sannan yayi musu umurni akan suyiwa Hassan ɗa'a kuma suyi masa biyayya!
A nan ne Hassan ya tashi tsaye sai yacewa Malamin:
Shin zai iya yiwuwa inyi tambaya?
Malami yacewa Hassan Bismillah, zaka iya tambayar ka!
Sai Hassan yace: Kunce Annabi (S) yabar duniya ba tare da ya ayyana kalifa a bayansa ba, shin Annabi (S) bai kai malaman mu (Masu girma) ilimi da tsantseni da sanin ya kamata bane? Tunda kunce bai ayyana wanda zaici gaba da tafiyantar da al'amuran addini a bayan sa ba, kuma bai sanya wanda zai ci gaba da hana rikici tsakanin al'ummar musulmi da daular ubangiji a bayansa ba?!!
Dukda cewa malam kasan zaka dawo anjima amma ka daura ni a matsayin kalifa a bayan ka, to taya Annabi (S) da yasan idan ya bar duniya bazai dawo ba yabar al'ummar musulmi haka nan kara zube ba kalifa?
Nan wannan Malamin yayi shiru na ɗan wani lokaci, yana ta tunanin hanyar da zai ɓullo wa Hassan, da yaga bashi da amsar da zai bashi sai ya waske ta hanyar tura Hassan wajen shugaban makaranta domin a azabtar da shi!!!
Bayan an kai Hassan wajen shugaban makaranta sai ya bukaci Hassan ya tafi gida domin ya taho da majiɓancin lamarin shi,
Washe gari sai ga Hassan yazo tare da abokin shi na makaranta,
Nan shugaban makaranta yayi mamaki, yace: Hassan me yasa baka taho da majibancin lamarin ka ba?
Sai Hassan yace: Wannan shine Majiɓancin lamari na.
Sai shugaban makaranta ya fusata, yace: Ina nufin Majibancin lamarin ka, ma'ana wanda yake da wilaya akan ka, kamar mahaifin ka...
A nanne Hassan yace: A yanzu kace: Majiɓancin lamari shine wanda yake da wilaya akai na, kamar mahaifin na...
Amma a lokacin da Annabi Muhammad (S) yace: "Shin ba nine mafifici akan muminai daga kawunan ku ba? Sai sahabbai suka ce haƙiƙa hakane, sai yace: wanda duk na zamo shugaba a gare shi, ya riƙi wannan Alin a matsayin shugaba a gare shi,
Sai ku kuma kuka ce: Ai (maula) Annabi (S) yana nufin Abota ne, da kyakkyawan alaqar dake tsakanin shi da Ali, shin ba haka bane?
Wannan tasa yanzu nazo muku da abokina wanda nake son shi, kuma muke da kyakkyawan alaka da shi, to meyasa ba zaku karɓe shi a matsayin Majibancin lamari na ba?
Nan fa shugaban makaranta yayi shuru, domin bai san amsar da zai bawa Hassan ba!
Akwai Darasi Ga Masu Hankali!
Ya Allah ka sanya mu daga cikin masu wulaya wa AHLULBAITI (AS) ka kyautata makomar mu.
✍️ Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment