Shah na Iran ya kore shi,
jam’iyyar Ba’ath ta Iraki itama haka,
gwamnatin Kuwait ta hana shi shiga kasarta.
Marji'in addini ne, abin so ga al’umma,
Yana cikin hamada shi kadai tare da Sayyid Ahmad ɗansa.
Dukda haka bai karaya ba, ya dogara da Allah.
An ɗauki wannan hoton na alwalarsa,
domin tarihi ya sani cewa:
idan gwamnatoci sun tasar maka, hanyoyi suka rufe,
kuma miyagun ƙarfi suka haɗu domin gamawa da kai —
idan Allah yana tare da kai,
zaka kasance cikin natsuwa ba tare da tsoro ba,
Allah ya yi maka rahama ya Imamu (QS).
Comments
Post a Comment