🌑 Daren Bankwana – Tare Da Ummul Masa'ib Sayyida Zainab (AS).
A daren goma ga watan Muharram – Daren Bankwana, ranar kafin yaƙin Karbala – Su Sayyida Zainab sun cika da baƙin ciki, da jiran irin ƙaddarar da zata faru. Wannan dare shi ne lokacin da Sayyida Zainab (عليها السلام) ta fuskanci mafificin nauyin rayuwa, da azaba da jimami.á
Shine dare na karshe da zata ga fuskar manyan ‘yan uwanta,
Dare ne da ke ƙunshe da ƙunci da baƙin ciki da rabuwa da ƙaunar da babu kamarsa.
💔 Aƙila Zainab da Imam Husain (AS): Bankwana Na Ƙarshe
A cikin duhun dare, Sayyida Zainab ta tunkari ɗan uwanta Imam Husain tana kuka, zuciyarta cike da firgici da damuwa tace:
"Yā Aba Abdillah... shin wannan shi ne bankwana na karshe?
Shin daga gobe zan zama cikin kaɗaici ba tare da kai ba?
Shin daga gobe zanci gaba da ɗaukan yaran da suka rasa iyayensu (marayu)?
Imam Husain (عليه السلام) ya rungume ta da ƙauna, yana cewa:
"Kiyi haƙuri ya Zainab… akwai babban jarabawa a gobe, amma nasara tana tare da juriya da tawakkali. Kin kasance abin alfahari ga Ahlulbayt, kici gaba da kasancewa a hakan."
🔥 Lokacin da zuciya ke kuka
Wannan dare ba kawai dare ne na jimami da kuka ba, amma dare ne da Sayyida Zainab ta ji kamar zuciyarta za ta fashe, saboda yadda musibu suka taru sukai mata yawa.
Tana ganin:
Yara wasu daga ƙananan yara suna barci cikin ɗaci, ba tare da sanin cewa gobe za su zama marayu ba, wasu kuna suna ta kiran ƙishirwa! ƙishirwa!! ƙishirwa!!!
Kamar su Ruqayya, da Ali Asghar, da Sakina...
Jaruman Ahlulbayt da Sahabban Imam Hussain (AS) suna shirin fuskantar shahada, amma ba a san su da fargaba ba, sai tawakkali, da jin yaƙinin zasuyi nasara.
🕯️ Sayyida Zainab: Tutar Karfafa Imani
Daren Bankwana ya tabbatar da cewa Sayyida Zainab ba mace ce kamar sauran mata gama gari ba — ita tutar karfafa ce, uwar karimci, madubin juriya da jarumta.
Ta ƙaddara tun kafin hasken safiya ya fito, cewa:
"Duk da wutar kaddara, ba zan bar tutar Husain (ع) ta faɗi ba!"
🌌 Wani Zubi Na Zuciya, Ta Kasance A Irin Wannan Dare Na Goma Tana Waƙe Tana Cewa:
Ya dare, kada ka ƙare da wuri...
Ka bar ni in ƙara kallon fuskar ɗan uwana,
Ka bar ni in rungumi Ali Asghar rumguma na ƙarshe,
Ka bar ni in sumbaci Raƙayya kafin safiya ta iso.
Ka bar ni in yi kuka da gwiwata akan ƙasa...
Domin gobe, bansani ba ko zan sami damar hakan..."
Ya dare… ka tsawaita!
Na rasa Abbas,
Na rasa Ali Akbar, tauraron fata,
Na rasa yara da suke dariya yau, gobe kuma su zama abin kuka.
Na kalli Ruqayya tana barci a ƙurya,
Na sumbaci kumatun Ali Asghar,
Ina jin numfashinsu, amma zuciyata tana ɓari —
Domin ban san ko zan sake jin hakan bayan gobe ba.
Ya dare... ka zamo shaida!
Husain yana ibada, yana salla,
Yana addu'a ga Allah da hawaye a fuskarsa,
Amma zuciyarsa cike take da tawakkali da yarda.
Na tunkare shi…
Na kalli ɗan uwana wanda na tashi da shi,
Na ce masa: "Waye zai zama jinina bayan kai?"
Sai ya ce da ni:
"Zainab! Ke ce amana, ke ce mai ɗaukar tutar juriya.
Ki zama kamar bango ga waɗanda suka rage!"
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un...
Ya dare… ba zan manta da kai ba.
Ka shaida cewa karfin mata ba ya karewa,
Ka shaida cewa Zainab ta dora nauyin Ahlulbayt a kafaɗarta.
Ka shaida cewa, da safe, duniya za ta canza…
Amma sunan Husain zai rayu har abada!
Haka ɓangarensu Imam Hussain (AS) suka ci gaba da shiri, daga masu sallan bankwana, sai masu tasbihi da istigfari da salatin Annabi fuskantarsu hawaye na kwaranya.
Ɗaya ɓangaren na maƙiyawa kuma suna ta shewa, suna ihu, suna buga ganga, suna ta ciye-ciye da shaye shaye da shirin sheƙar da jinin Ahlulbaiti a gobe Ashura (Goma Ga Watan Almuharram). Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un
Sat, Jul 5,
2025.
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment