Halin Ƙunci Da Tashin Hankali Da Al-ummar Gaza Ke Ciki.
Al-ummar Gaza na fuskantar wani mummunan hali na yunwa da tashin hankali, sakamakon hare-haren da HKI ke kaiwa ba kakkautawa tun watanni da suka gabata. Yara da mata da tsofaffi na mutuwa kowace rana saboda yunwa, rashin magunguna, da rushewar cibiyoyin lafiya da rashin abinci. An kulle hanyoyin shigar kayan agaji gaba ɗaya, lamarin da ya jefa al’ummar cikin mummunan hali.
Duk da wannan bala’i mai tsanani, yawancin ƙasashen Larabawa na kallon abin yana faruwa ba tare da matakin taimako mai ma’ana ba. Wasu daga cikinsu ma suna toshe hanyoyin agaji, yayin da wasu ke nuna shiru tamkar ba su da alhakin addini ko na ɗan Adam. Wannan ya jefa al’umma cikin ƙunci, tare da nuna gazawar haɗin kan Larabawa da kuma ƙarancin damuwa da rayukan ‘yan’uwa musulmi a Gaza.
Halin Gaza darasi ne ga duniya baki ɗaya: ko da akwai 'yan'uwa a addini da harshe, sai an sami mutanen da ke da haƙiƙanin damuwa da shiri don taimakawa, in ba haka ba, zalunci zai ci gaba da yin katutu.
Na karanta a wani jarida cewa: "Hatta tsuntsaye sun bar yankin Gaza saboda rashin abinci da rasin ruwa" Al-ummar Musulmi wannan wane irin bala'i ne?
Shi yasa idan baka da abinda zaka taimaka musu aƙalla ka taimaka wajen wayar da kan jama'a ta Hanyar rubutu a kafafen sada zumunta, Allah ya kawo musu ɗauki.
Fri, Jul 25,
2025.
Emran Darussalam.
Comments
Post a Comment