HATSARIN DAKE CIKIN KETA ALFARMAR MARJI'IYYA.
Sayyid Muhammad Sadiq Rowhani (DZ) yace: " ya kamata ƴayan mu maza da mata su sani cewa: cin zarafin Manyan Marji'ai "Daga ko waye hakan ya fito" alama ce ta taɓewa, ko ince girman kai da bin soye-soyen zuciya, sannan ɗaukan bashi ne a wajen Allah maɗaukaki, kuma mun sani cewa: duk wani mai wuce gona da iri akan Marji'iyya (mai albarka) wannan alama ce ta farkon faɗawa hawuya da kaucewa daga hanya, muminai ku kiyaye faɗawa cikin wannan sashe da bazaku iya tsayawa akan ƙafafun ku ba ranar kiyama.
Ya Allah ka tsare mu.
24/07/2022
Comments
Post a Comment