A duk sanda zuciyarku taji tana kewar ganin Imamul-Hujjah (Atfs) to ku dubi shafukan Alkur'ani... Sheikh Muhammad Taƙi Bahja (QS).
Imam al-Sadiq (as) ya ce: “Al-Qur’ani alkawarin Allah ne ga halittunsa, don haka ya kamata Musulmi ya duba cikin wannan alkawari, kuma ya karanta daga cikinsa kowace rana ayoyi hamsin (50) (alal aƙall)... Alkafi Juz'i na 2, Shafi na 609.
Imam Ali (AS) Yace: “Ku koyi karatun Al-Qur’ani, domin shi ne mafi kyawun zance. Ku zurfafa ilimi a cikinsa... Ku nemi warkarwa da haskensa, domin shi ne warakar zukata, Kuma ku kyautata karanta shi, domin shi ne mafi amfanin labarai.”
📚 Nahjul Balagha, Hikima ta 110.
Ya Allah Ka Bamu Ikon Karanta Littafinka A Koda Yaushe.
Mon, Jul 28
2025,
Comments
Post a Comment