Ayyukan daren farko na watan Rajab: 1– Wanka (Gusl): An rawaito daga Manzon Allah (SAW) cewa: “Duk wanda ya samu watan Rajab, ya yi wanka a farkonsa, tsakiyarsa da ƙarshensa, zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.” 2– Raya daren (ibada a daren): Wannan na daga cikin darare huɗu da ake ƙarfafa mustahabbancin rayar da su. An rawaito daga Abu Abdullahi (AS), daga mahaifinsa, daga kakansa, daga Ali (AS) cewa ya ce: “Yana so ya keɓe kansa a darare huɗu cikin shekara: daren farko na Rajab, daren tsakiyar Sha’aban, daren Idin Fitr, da daren Idin layya.” 3– Addu’a lokacin ganin jinjirin wata: اللّهُمَّ أَهِلَّهُ عَلّيْنا بالأمْنِ وَالإيْمانِ وَالسَّلامَةِ وَالإسْلامِ رَبِّي وَرَبُّكَ الله عَزَّ وَجَلَّ. Kuma Manzon Allah (SAW) idan ya ga jinjirin Rajab yana cewa: اللّهُمَّ بارِكْ لَنا فِي رَجَبٍ وَشَعْبانَ وَبَلِّغْنا شَهْرَ رَمَضانَ وَأَعِنَّا عَلى الصِيامِ وَالقِيامِ وَحِفْظِ اللّسانِ وَغَضِّ البَصَرِ وَلا تَجْعَلْ حَظَّنا مِنْهُ الجُوعَ وَالعَطَشَ. Sal...