Faƙihin Malamin nan Ayatullahi Shaykh Lutfullah as-Safi al-Gulbaygani (QS) ya ce:
Al-Intizār (Jira) makaranta ce kuma babbar jami’a ta tsarkake zuciya da gina kai da ruhi. Dole ne ga wanda ya danganta kansa da wannan manhaji ya zamto tsayayye tsayuwa da ƙarfi, kuma ya zamto mai aikata abin da ke cikin Du'a al-Ahd a inda muke cewa: mu “masu gaggawar zuwa gare shi ne wajen biyan bukatunsa …”; wato (mai jiran zuwan Imam Mahdi) wajibi ne ya yi ƙoƙari sosai wajen biyan bukatun Waliyul Asr, Allah Ya gaggauta bayyanarSa.
Masu jiran Imam al-Hujja (Atfs) su kiyaye addininsu, su tsare iyalansu da matasansu daga karkacewa da ɓata, kuma su himmatu wajen biyan bukatun muminai; domin a gaskiya waɗannan su ne bukatun Imamin Zamansu (Atfs).
Ayyuka A Lokacin Intizar:
- Tsayuwa kan Sallar farilla
Yin salla a kan lokaci, musamman sallar jam’i idan akwai dama.
Domin salla ita ce ginshiƙin addini kuma tana tsare mutum daga karkacewa.
- Addu’a musamman domin gaggauta bayyanarsa:
Du'a al-Faraj: “Allahumma kun li-waliyyika…”
Du'a al-‘Ahd (musamman da safe)
Ziyarat Āli Yāsīn Waɗannan addu’o’i suna sabunta alaka da Imam (A.S.).
- Kiyaye addini da tsoron Allah (taqwa)
Gujewa haram, cin halal, gaskiya, amana, da adalci.
Imam Mahadi (A.S.) yana bukatar mabiya masu tsafta ta zuciya da aiki.
- Gyaran kai da tarbiyyar ɗabi’a
Hakuri, tawali’u, kyakkyawan hali.
Intizār makaranta ce ta gina mutum kafin zuwan Imam.
- Hidimtawa jama’a (cika bukatun muminai)
Taimakon talakawa, warware matsalolin jama’a, da yin hidima ga al’umma.
A ruwayoyi: biyan bukatar mumini kamar biyan bukatar Imam ne.
- Ilmi da fahimtar addini
Koyo da koyar da ilimin Qur’ani da Ahlul Baiti (A.S.).
Domin masu jiran Imam dole ne su kasance masu basira, ba jahilai ba.
- Al-amru bil ma‘rūf wa nahyi ‘anil munkar
Kira zuwa ga alheri da hana mummuna cikin hikima da kyakkyawan salo.
- Zaman shiri da aiki, ba zaman jira kawai ba
Aiki don gyaran kai, iyali, da al’umma.
Jiran Imam ba zama ne da sakaci ba, jiran aiki ne.
Ya Allah Ka Bamu Iko.
Wed, Dec 25,
2024.
Comments
Post a Comment