🌙 Falalar Azumin Watan Sha‘abān daga Ahlul Baiti (A.S).
Sha‘abān watan Annabi (S).
Imam Ali (A.S) ya ruwaito cewa Manzon Allah (S) ya ce:
“Sha‘abān watana ne, wanda ya yi azumi rana ɗaya a cikinsa, Aljanna ta wajaba a gare shi.”
📚 Duba littafin "Wasā’ilu sh-Shī‘a"
Azumi a Sha‘abān yana jawo gafarar zunubai.
Imam Ja‘afar As-Sadiq (A.S) ya ce:
“Duk wanda ya yi azumi a kwanaki uku na ƙarshen watan Sha‘abān, Allah zai rubuta masa azumin wata biyu a jere.”
📚 Duba littafin "Bihārul Anwār"
Sha‘abān shiri ne ga Ramadān.
Imam Ali (A.S) ya ce:
“Manzon Allah (S) yana yawaita azumi a watan Sha‘abān, yana haɗa shi da Ramadān.”
📚 Duba littafin "Nahjul Balāgha" (ma’ana daga ruwayoyi).
Azumin Sha‘abān yana horar da rai, yana tsaftace zuciya, kuma yana shirya bawa ga Ramadān.
Azumin Sha‘abān kariya ce daga wuta.
Imam Ar-Ridha (A.S) ya ce:
“Duk wanda ya yi azumi a Sha‘abān saboda ƙaunar Annabi (S), Allah zai ƙaunace shi, Ya kuma kare shi daga wutar Jahannama.”
📚 Duba littafin "Bihārul Anwār"
Sha‘abān wata ne na rahama da salati ga Annabi (S)
Imam As-Sadiq (A.S) ya ce:
“Sha‘abān wata ne da ake yawaita salati ga Annabi (S), kuma azuminsa yana ƙara kusanci ga Allah.”
Ya Allah Ka Bamu Iko
21/01/2026,
Comments
Post a Comment