Dukkanin cikar kamala da darajoji da aka samu a wajen wanzuwar darajar Manzon Allah ﷺ da iyalansa, Sayyida Khadijah da Siddiqah Al-Kubra Fatimah Az-Zahra, da Amirul Mumineen (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su gaba ɗaya), duka akwai su kuma sun bayyana a wanzuwar darajar Sayyida Zainab (tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta). Manzon Allah ﷺ da iyalansa sun ce duk wanda ya yi kuka a kan wannan jaruma, to kamar ya yi kuka ne a kan 'yan uwanta biyu, Imam Hasan da Husain (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su). Ma'ana, hawaye guda daya a kan juyayin Sayyida Zainab yana daidai ne da kuka a kan juyayin Imamai biyu ma'asumai (tsira da amincin Allah su tabbata a gare su gaba ɗaya).
15 Ga Watan Rajab Shahadan Sayyida Zainab, Ya Allah Ka Ƙara Mana Ƙaunarta.
Sayyid Ahmad Al-Musawi.
Comments
Post a Comment